Zaman ɗar-ɗar a Rivers yayinda Kotu ta bada Umarnin tsare Ɗan Takarar Gwamna ga Ƴan Sanda
Ana tsare da Ɗan Majalisar Tarayya kuma Ɗan Takarar Gwamna a Jam’iyyar PDP a Jahar Rivers Farah Dagogo.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ɗan Takarar Gwamnan Katsina ya fara tsorata, Yace zai bi duk wanda ya samu nasara, bashi ba
Wata Kotun Majistare dake zaman ta a Fatakwal dake ƙarƙashin jagorancin Chief Majistare Amadi Nna ya bada umarnin, biyo bayan kama shi da akayi a ranar Juma’a.
Dagogo yana wakiltar Degema/Bonny a Majalisar Wakilai ta Ƙasa.
Dagogo bai halarci tantancewar ƴan takarar masu neman Gwamna a Shekarar 2023 sakamakon kama shi da akayi a ranar Alhamis.
Comments 1