Ƴan Daba sun Jikkata Mambobin PDP suna Tsaka da Taro a Kogi
Kimanin mutane goma sun Jikkata, bayan bata gari sun shiga wurin da ake taron Matasan Jam’iyyar PDP a Ologba na Ƙaramar Hukumar Dekina a Jahar Kogi.
A cewar wanda ya shaida lamarin, sun yi amfani da bindigu, wuƙa ƙe, da sauran makamai masu hatsari a lokacin kai hari.
Daily Post ya gano cewa ɓata garin sun kuma ƙona Motoci da Mashina na wasu ƴan Jam’iyyar PDP. Haka zalika, sun ƙone gidan Matashin Jam’iyyar.
“”Akwai zaman ɗar-ɗar a Ƙaramar Hukumar Dekina. Ƴan Dabar sun zo inda Matasan PDP ke taro a jiya a Ologba, sun lalata kayayyaki, sun ƙone Motoci da Mashina,” Inji wani.
A watan Nuwamba na Shekarar 2019, Shugabar Matar Jam’iyyar PDP a Mazaɓar Ochadamu ta Ƙaramar Hukumar Ofu Mrs Acheju Abu, an Kashe ta daga wasu ƴan siyasa, da suka ƙone ta a gidan ta da ranta.
Dukkanin ƙoƙarin jin tabakin Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan Sandan Jahar Kogi SP William Ovye Aya. Bai ɗaga kira ba, bai maido da saƙonnin da aka tura mashi ba.