Ƴan Majalisar Yobe Sun yi Kakkausan Gargaɗi ga Gwamna Buni akan yawaitar Ambaliyar Ruwa da ake samu
Majalisar Dokokin jihar Yobe tayi kira ga bangaren zartaswa a jihar da su kara kai dauki ga wadanda bala’in ambaliyar ruwa ya shafa a fadin jihar.
Majalisar ta bayar da wannan umarni ne a wani kudiri na gaggawar da Ɗan majalisa mai wakiltar mazabar Jajere Hon. Chiroma Buba Mashio ya gabatar akan bukatar tallafawa wadanda bala’in ambaliyar ruwa ya rutsa dasu a jihar.
A nasu gudunmuwar daban-daban kan kudirin, mataimakin kakakin majalisar Hon. Mohammed Isa Bello, Shugaban Majalisar Hon. Bukar Mustapha, Hon. Abdullahi Adamu Bazuwa da Hon. Kachalla Ajiya Maina da sauran jama’a sun jajanta wa wadanda ambaliyar ta shafa tare da jaddada bukatar hukumar zartaswar jihar ta duba matsalolin da ake fama da su domin samun dauwamammen mafita ga bala’in da ke faruwa a jihar a kowace shekara.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu-Yanzu: Mayakan ISWAP Sun Yi Garkuwa Da Manoma A Borno
‘Yan majalisar, wadanda suka yi dogon bayani kan bala’in, sun ce ya janyo hasarar rayuka da barnata gonaki, gidaje da dukiyoyi na miliyoyin naira a mazabunsu da ke fadin jihar.
Sun kuma jaddada bukatar gwamnati ta umurci kwamitocin kula da tsaftar muhalli na kananan hukumomi da su share dukkan magudanun ruwa tare da gina wasu karin magudanan ruwa musamman a yankunan domin shawo kan matsalar ambaliyar ruwa a duk shekara.
Da yake jagorantar zaman, Kakakin Majalisar Rt. Hon. Ahmed Lawan Mirwa ya umurci kwamitocin majalissar kan muhalli da filaye da safiyo da su gana da ma’aikatar muhalli ta jiha da ma’aikatar yada labarai ta jihar Yobe (YOGIS), domin duba matsalar gina gidaje da zubar da shara a magudanan ruwa domin a samu matsala. mafita mai ɗorewa