Ƴan Majalisu sun buƙaci ƙarin shekarun aiki ga masu buƙata ta musamman daga 65, 70
Majalisar Wakilai ta Ƙasa a jiya tayi karatu na biyu akan wani ƙudiri dake neman ƙara wa’adin shekarun aiki na masu buƙata ta musamman daga shekaru 65 zuwa 70, ma’ana shekaru 40 a aiki.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sojojin Nijeriya Sun Sake Ceto Wata Ƴar Makarantar Chibo
Babajimi Benson ya gabatar da Ƙudirin, inda yace neman gyaran fuska ga ƙudirin na neman kawo yi mashi kwaskwarima.
Gyaran kamar yadda ya bayyana, zai ƙunshi shigar da ƙaramin sashe na 30(1) wanda ya buƙaci a kara wa’adin shekarun ajiye aiki daga 65 zuwa 70, ko kuma shekaru 40 a aiki, wanda wannan ne yazo farko.
Ya ce gyaran na biyu na neman tabbatar da cewa sai Shugaban Hukumar Kula da masu buƙata ta musamman, shine mutum wanda yake da dukkanin takardu a matsayin muƙamin.
Benson yace dalilan wannan Ƙudiri na sake yin gyara shine a tabbatar cewa masu buƙata ta musamman an kula dasu da adalci.
“Kuma zai basu dama wajen yanke hukunci akan dukkanin abubuwan da suke bukata. Wannan hanyoyin a manyan kasashe baza’a bar wa Najeriya ba”, Inji shi.