Guda cikin yan takarar Shugabancin kasar nan Chukwuemeka Nwajiuba ya ce yan kasar nan 3,150 ne suka hada masa Naira miliyan 100 domin ya siyan Fom din takarar shugaban kasa.
Chukwuemeka wanda shine tsohon karamin ministan Ilimi, ya kuma bayyana yadda wasu manoma doya a jihar Nassarawa suka hada masa akalla Doya 150, domin ya Siyar ya kara kudin kan wanda yake da su domin siyan Fom din takarar.
Wannan jawabi nasa ma zuwa ne bayan da rade radi ya cika gari cewa, wasu kusoshin Dillalan man fetur me suka siya masa Fom din, domin ya tsaya takarar shugaban kasar a zaben 2023.
Chukwuemeka dai guda ne cikin muƙarraban gwamnatin shugaban kasa Muhammad Buhari, wanda kuma tuni ya yi sallama da mukamin masa, domin tsayawa takarar kamar yadda doka ta tanada.
Ya kuma koka kan yadda wasu daga cikin yan siyasa suka mayar da harkar wata hanya ta samun kuɗi, wanda hakan ya sanya ba a samun damar Amfana daga gare su matsayin su ma shugabanni.