Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jihar Adamawa ya bayyana kwarin guiwar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, kuma tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, da cewa zata kaisu ga nasara a baɗi.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Fintri ya jaddada cewa 2023 ta zama abin koyi ga PDP kuma ‘yan Najeriya ba za su yafe wa jam’iyyar PDP ba, idan har jam’iyyar ta kasa lashe zaben shugaban kasa a 2023.
Fintiri ya bayyana haka ne a ranar Lahadin nan, a wata hira da manema labarai a filin jirgin sama na Yola, a lokacin da ya isa jihar bayan kammala aikin sulhu tsakanin gwamnan jihar Ribas, Nyeson Wike da jam’iyyar.
“Ina ganin 2023 ta PDP ce, Atiku da yardar Allah shi ne zai zama shugaban kasar nan kuma ‘yan Nijeriya ba za su yafe mana ba idan har muka kasa samar da shugaban kasar nan a 2023.
“Komai a karkashin gwamnatin APC ya wargaje, komai yana cikin rudani, ‘yan Najeriya da alama ba su fahimci inda suke ba.
“Muna tashi kowace safiya da yardar Allah. Don haka a matsayinmu na shugabanni, za mu tabbatar mun sanya komai a cikin wannan sulhu don ganin cewa Atiku da Wike sun dawo a matsayin jam’iyya daya tare kuma da hadin kai domin samun nasarar PDP a 2023,” inji shi.
Ya kuma bayyana cewa a yanzu shi ne shugaban kwamitin sulhu tsakanin Atiku da Wike, inda ya kara da cewa aikin da ya kai su jihar Rivers ya samu nasara.
Ya kamata ku dinga kyautata Zato ga Ƴan Fim – Jaruma Hannatu Bashir
“Sun fara magana kuma za su ci gaba da tattaunawa har sai an warware dukkan batutuwa cikin ruwan sanyi,” in ji shi.
A cewarsa, “Siyasa ta shafi mu’amala, tattaunawa da fahimtar juna.”
Ya ba da tabbacin cewa nan ba da jimawa ba za a kawo karshen sulhun tsakaninsu, kuma jam’iyyar za ta mayar da hankali wajen kwato Nijeriya da ‘yan Nijeriya daga gazawar shugabancin APC.