Shugaban Ƙungiyar Ƴan Aware na Ƙasar Yarbawa Sunday Igboho, yayi zargin cewa wasu ƴan siyasa na matsa mashi akan ya baiwa fadar shugaban ƙasa haƙuri.
Igboho yace wasu ƴan siyasa na matsa mashi, da matar shi akan ya sanya hannu akan wasu takardu da zasu yi amfani dasu, domin baiwa Fadar Shugaban Ƙasa haƙuri a madadin shi.
Dayake Jawabi a tabakin lauyan sa Yomi Alliyu yace duk wani takardu da aka ce shiya sanya hannu a bada haƙuri ba gaskiya bane ba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Cutar Amai Da Gudawa Ta Kama Mutane 90,890, Inda Jigawa, Yobe, Zamfara Suke Samun Allurar Rigakafin Ta
A cikin sanarwar da Alliyu ya sanyawa hannu, Igboho yace yana shan matsatsi daga wasu ƴan siyasa, da basu damu da halin da yake ciki ba a Jamhuriyar Benin.
Idan dai za’a iya tunawa ana tsare da Sunday Igboho a Jamhuriyar Benin biyo bayan kama shi da akayi a ƙasar.
An kama ɗan awaren a filin jirgin Cotonou a lokacin da yake ƙoƙarin barin ƙasar zuwa Germany.
Yadai tsere daga Najeriya bayan jami’an tsaro farin kaya na DSS, sun sanya shi a cikin jerin wanda suke nema ruwa jallo.
Haka zalika, DSS sun sanya Igboho cikin jerin wanda suke nema bayan sun samu makamai a gidan sa dake Ibadan, inda daga bisani ya ƙaryata mallakar makaman.