Wata budurwa ta bayyana ra’ayinta dangane da yadda ‘yan uwa da abokan arziki su ka mayar da kudi jigon rayuwa inda tace gara kayi ake da kaje. LIB ta ruwaito.
A cewarta, ta kula cewa gara ka dunkula kudi ka aika shi ga ‘yan uwanta akan ka wanke kafa ka kai musu ziyara duk nisan da su ke dashi daga inda kake.
Kamar yadda budurwar, wacce take zama a kasar waje ta bayyana, a halin da musamman ‘yan Najeriya su je, sun fi daraja kudi akan zumunci ko kuma ziyara.
A wallafar da General_Oluchi tayi a shafinta na Twitter, ta ce son kan ‘yan Najeriya ya kai ga sun fi nuna damuwarsu akan kudi akan lafiyar dan’uwansu.
Ta bayyana hakan ne bisa abinda ta kula ya faru da ita a kan ta. Ta ce da zarar ka tafi kasar waje, burin duk ‘yan uwa ka dinga tura musu kudi a maimakon su nemi sanin halin da kake ciki.
KU KARANTA: APC da PDP na shirin amfani da kuɗi don siyan yan Najeriya a 2023 – NNPP
Jam’iyyar NNPP, ta zargi jam’iyyar APC, da PDP, da shirin sayen ‘yan Najeriya, kamar yadda ake Siyen raguna a kasuwa lokacin layya.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa jamiyyar ta ce suna aiwatar da wannan shirin ne a zaben 2023 mai zuwa.
Dan takarar gwamna na jam’iyyar NNPP a jihar Jigawa, Malam Aminu Ibrahim Ringim, ya bayyana haka a ranar Asabar a wurin kaddamar da ofishin jam’iyyar da ke gundumar Aujara a karamar hukumar Jahun.
Ya ce APC da PDP na shirin yin amfani da kudin wajen siyan kuri’u daga hannun ‘yan Najeriya a zaben 2023 mai zuwa.