Wani bidiyon bikin wani ɗan Najeriya da masoyiyar sa ƴar ƙasar Indiya ya bazu a shafin sada zumunta na TikTok.
Bidiyon wanda wani mai amfani da sunan @grakeshots a TikTok ya sanya, mutane da dama sun kalle yayin da suke taya masoyan biyu murna. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
KU KARANTA KUMA: Ƙarancin kuɗi: Yadda ƴan Najeriya suka koma bani gishiri in baka manda
Cikin shigar su ta ƴan ƙasar Indiya, masoyan biyu an yi auren su a wani gagarumin shagalin biki irin wanda ake gani a finafinan Indiya.
Amaryar na sanye da sarƙokin masu ɗan karen kyau, sannan duk jikinta a lulluɓe yake in banda fuskarta da hannuwanta.
Mutane da dama sun bayyana ra’ayoyin kan wannan auren na masoyan guda biyu, inda da yawa daga ciki suka yaba musu.
Ku kalli bidiyon a nan
Ga kaɗan daga cikin waɗanda Dimokuradiyya ta tattaro:
user2744256581533 ya rubuta:
“Wow wannan yayi kyau sosai. Ina taya ku murna.”
FEEZA ta rubuta:
“Dole kun sha wuya kafin zuwan wannan ranar, nayi muku farin ciki sannan ina taya ku murna.”
vendettalady5 ta rubuta:
“Gwanin ban sha’awa. Muna buƙatar mu haɗa kawunan mu, dukkanin mu ƴan Adam ne. Yana da kyau a nunawa duniya cewa so ba ruwan shi da kala, Allah ya albarkace ku.”
Tirƙashi: Bidiyon Matashi Mai Aski Da Cokali Ya Janyo Cece-Kuce
A wani labarin na daban kuma, bidiyon wani matashi mai aski da cokali ya janyo cece-kuce
Wani matashi wanda yayi amfani da cokali ya yiwa wani yaro aski, ya ƙaraɗe shafukan sada zumunta bayan bayyanar bidiyon sa a Instagram.
An yiwa yaron aski mai kyau da cokali a cikin wani ɗan gajeran bidiyo wanda @jskvibes ya sanya a Instagram.