Ɗangote na raba sinƙin biredi dubu 35,000 kullum a Kano da Legas
Attajirin da yafi kowa Arziki a Nahiyar Afirka Alhaji Aliko Ɗangote a halin yanzu yana raba sinƙin biredi dubu 20,000 kullum a jihar Kano, a yayin da yake raba guda dubu 15,000 a jihar Legas.
Haka zalika, Alhaji Aliko Dangote, ta hannun gidauniyar Aliko Dangote, ya kaddamar da rabon abinci kyauta ga al’ummar Musulmi mutum dubu 10,000 a jihar Kano, jiharsa ta asali.
KARANTA WANNAN LABARIN:Ƙungiyar Likitoci ta nesanta kanta da likitan bogi
Har ila yau, gidauniyar tana irin wannan aikin ta hanyar raba buhunan shinkafa miliyan daya da kudinsu ya haura Naira biliyan 13 a fadin jihohi 36 na tarayya da Abuja domin rage yunwa a kasar.
Manufar ita ce a sassauta wa miliyoyin ƴan Najeriya kan wahala da suke sha, sakamakon kalubalen tattalin arziki a kasar.
Wannan ƙari bisa ga rabon biredi 20,000 a kullum ga mazauna Kano da kuma 15,000 a kullum ga mazauna Legas, abincin da aka fara kuma ya dore tun 2020 a lokacin COVID.
Abincin da ake rarrabawa a cikin watan ramadan kyauta ya haɗa da jollof rice, farar shinkafa da miya, da dafaffiyar taliya, wake da kaza da naman sa, tare da kwalbar ruwa ga kowane mutum.
Akwai kuma raba abinci a masallatan Juma’a da tituna da gidajen yari da gidajen marayu da gidan yari da sauran wurare a cikin birnin Kano da kewaye.
Wani wanda ya ci gajiyar abincin mai suna Musa Maikatako mazaunin Tarauni ya nuna jin dadinsa da wannan karimcin inda ya ce ya taimaka masa wajen yin buda baki cikin sauki.
Maikatako, wanda yake cikin farin ciki, ya ce cin abinci na kyauta zai magance wahalhalun da jama’a da dama da za su yi buda baki da ruwa kawai, ba tare da abinci ba, la’akari da halin kuncin da ‘yan Nijeriya ke ciki.
“Ba zan iya bayyana irin farin cikin da nake ciki ba, wannan abincin zai taimaka matuka wajen taimaka wa talakawa su samu abin da za su yi buda baki a kalla da abinci mai kauri.
“Na san mutane da yawa a jihar nan wadanda za su yi buda baki da ruwa kawai. Don haka wannan abincin ya kawo sauki,” in ji shi.
Da yake nuna farin cikinsa, Maikatako ya nuna godiya ga gidauniyar Dangote bisa wannan karimcin, inda ya yi addu’ar Allah ya kara masa arziki, ya kuma ci gaba da sanya albarka a kasuwancinsa.
Wata wadda ta ci gajiyar tallafin, Hajiya Inna Tukur, ta bayyana jin dadin ta da rabon abincin, wanda a cewarta Gidauniyar Aliko Dangote ta kawo mata dauki.
Cewar Inna, ta yi farin ciki da an ba ta abinci mai daɗi kyauta a cikin yanayin da ake ciki.
“A cikin wannan wahalhalun da muke samu ko da sau biyu a rana muna wahalar cin abinci, amma wani ya gabatar mani da wannan abincin mai dadi, abin mamaki ne.
“Ba abin da zan ce sai dai in yi godiya ga ku da Aliko Dangote, ina rokon Allah Ya kara muku albarka.”
Baya ga rabon biredi da aka yi shekara 4 kyauta, an shafe sama da shekaru 30 ana ci gaba da ciyar da mabukata a Kano cikin nutsuwa da Aliko Dangote ya yi.
Wannan ciyarwa tana ciyar da ƴan Kano a ƙalla dubu 10,000 a cikin shekaru 30 da suka gabata.