In kun sake ni, cikin mintuna 2 zan kawo ƙarshen rashin tsaro a Kudu maso Gabas – Nnamdi Kanu
Shugaban masu fafutukar kafa kasar Biafra, IPOB, Nnamdi Kanu, ya sha alwashin kawo karshen rashin tsaro a yankin Kudu maso Gabas cikin mintuna biyu, idan aka sako shi daga inda yake a tsare.
Kanu ya ce a yankin Kudu maso Gabas babu wanda zai iya yin tir da umarninsa dangane da matsalar tsaro a yankin.
KARANTA WANNAN LABARIN:Ba za a mayar da kai daga hannun DSS zuwa kurkukun Kuje ba – Kotu ga Nnamdi Kanu
Fusataccen mai fafutukar kafa kasar Biafra ya yi magana ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a harabar babbar kotun tarayya da ke Abuja ranar Talata.
Kanu ya ce, “Ina zargin cewa wasu mutane a gwamnati suna samun kudi ne saboda rashin tsaro a yankin Kudu maso Gabas; sun san da zarar Nnamdi Kanu ya fita waje, nan da minti biyu, wannan shirmen zai tsaya.
“Wane wawan da zai iya canza umarni na a Kudu maso Gabas? Babu wanda zai iya. Ni Nnamdi Kanu, bari na fita daga wannan shirmen, kuma nan da minti biyu za a samu zaman lafiya a Kudu maso Gabas.”
Tun da farko, Mai shari’a Binta Nyako ta ki amincewa da bukatar Kanu na neman beli.
Sai dai alkalin kotun ya bayar da umarnin a gaggauta sauraren karar da ta shafi Kanu, wanda ke fuskantar tuhume-tuhume da suka shafi ta’addanci da kuma cin amanar kasa.
Kanu, wanda aka gurfanar da shi a gaban kotu a ranar Talata, yana hannun jami’an tsaro na farin kaya, DSS, tun bayan kama shi a watan Yunin 2021.
A wani labarin kuma:Ɗangote na raba sinƙin biredi dubu 35,000 kullum a Kano da Legas
Kungiyar likitocin Najeriya NMA reshen jihar Ekiti, ta nesan ta kanta da wani da ake zargin likitan jabu ne, Olalekan Timothy Fasipe, wanda aka kama a kwanakin baya bisa zarginsa da yin jabun takardar shaidar rijistar sa da kungiyar likitoci da hakori ta Najeriya, MDCN.
Olalekan, wanda ma’aikaci ne a Hukumar Kula da Asibitin Jihar Ekiti, ya kasance yana nuna kansa a matsayin kwararren likita ba tare da takardar shaidar cancanta ba.