Ɗaruruwan Ɗalibai sun tsallake rijiya da baya, bayan Gobara ta tashi a Makarantar Enugu
Ɗaruruwan Ɗalibai na Kwalejin Ilmi suka tsere wa gobara a ranar Alhamis, a lokacin da wuta ta barke a ɗakin kwanan ɗalibai.
Makarantar tana nan kusa da shirin ilmin Ɗalibai na Jami’ar Jahar Enugu, kusa da mahadar Nkpokiti a Enugu.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sassan Titin Kaduna Zuwa Zariya Zai Kammala Nan Da Watanni 6 – Gwamnatin Tarayya
Ɗalibai da dama sun Jikkata a lokacin da Ɗalibai suka ruga a yayinda Gobarar ta ɓarke.
Akwai bayanai masu karo da juna akan yadda wutar ta faru.
A yayinda wasu suka ce gobarar ta faru ne a dalilin Barin kayayyakin wutar lantarki da wata Daliba ta bari jone, ta tafi aji.
Duk da babu rayuwar da aka rasa, an gano cewa wutar ta lalata rufin gini, da sili, da kofofi, da kuɗin yakai Naira Miliyan 30.
Wutar an gano cewa ta ƙone wasu takardu na Ɗaliban.
Wasu malamai da suka yi jawabi akan yanayin lamarin, sun ce taimakon da Hukumar kashe Gobara ta kawo shiya hana ɗakin kwanan ya ƙone