2022 UTME: Ɗalibai 378,639 ne kawai suka samu maki sama da 200 – JAMB
Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jami’a ta JAMB a ranar Alhamis ta bayyana cewa Ɗalibai 378,639 ne kacal daga cikin 1,761,338 da suka rubuta jarrabawar JAMB ta 2022 suka samu maki 200 zuwa sama.
Magatakardar JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede ne ya bayyana hakan a yayin taron tsare-tsare na Shekarar 2022.
KARANTA WANNAN LABARIN: An Sake Maido Da Wutar Lantarki A Kasa Baki Daya Bayan Daukewar Wutar — TCN
A baya dai PUNCH ta ruwaito cewa Oloyede ya bayyana cewa ɗan asalin jihar Ekiti ya samu maki mafi girma a jarabawar UTME ta 2022 da hukumar ta gudanar.
Yayin da yake ba da ƙarin kididdiga na jarrabawar 2022, Oloyede ya lura cewa Ɗalibai 378,639 sun sami maki sama da 200; wasu 520,596 ne suka samu maki 190 zuwa sama; 704,991 sun samu maki 180 zuwa sama; sai Ɗalibai 934,103 sun samu maki 170 da sama; a yayinda 1,192,05 suma sun samu maki 160 Zuwa Sama.
Da yake ƙarin haske, Oloyede ya lura cewa hukumar ta ba Dalibai masu jiran sakamako damar rubuta Jarabawar UTME na 2022.
“JAMB ta ba da damar masu jiran sakamako su yi rajista da zama na UTME na 2022.
Ba za a iya la’akari da waɗannan Ɗalibai ba za’a basu guraben Karatu suna jiran sakamako ba.
Dole ne su gabatar da sakamakon O’level kafin bada guraben karatun.