Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta INEC Farfesa Mahmood Yakubu a ranar Litinin yasha alwashin ƙirga duk ƙuri’un da aka kaɗa a zaɓen Gwamnan Jahar Ekiti na ranar 18 ga watan Yuni.
Yakubu ya bayyana cewar Hukumar zata kasance tsaka-tsakiya, tare da bin dokokin hukumar na tabbatar da cewa ta yi zabe mai inganci.
KARANTA WANNAN LABARIN: Buhari Ya Tafi Birnin Madrid Na ƙasar Sipaniya domin ziyarar aiki
Shugaban Hukumar a Ado Ekiti a ranar Talata, ya bayyana haka a Jahar Ekiti a lokacin taro da masu ruwa da tsaki, gabanin zaɓen 18 ga watan yunin Shekarar 2022 na Gwamna a Jahar.
Dayake jawabi ga Saraken, Yakubu yace kimanin masu zabe 989,202 aka yiwa rajista a Ekiti, a yayin da kimanin mutane 740,000 suka karɓi Katin Zaɓe na Dindin.
Shugaban Hukumar ya bayyana cewar Hukumar zata gudanar da zaɓen Gwamnan dana ƴan Majalisun Jahar.
“Ina so in tabbatar wa da masu zaɓe cewa za’a ƙirga ƙuri’un su. Zan tattauna da masu ruwa da tsaki akan yanda za’a gudanar da zaɓe na kwanciyar hankali a Jahar.