Babban Mai bada Shawara akan sadarwa na shugaban Bankin Cigaban Afirka Akinwunmi Adesina, Victor Oladokun ya bayyana cewa “ba gaskiya bane” akan cewa ya Adesina ya zaɓi Bola Tinubu a matsayin ɗan takarar shugaban Ƙasa.
Victor Oladokun a lokacin da yake musanta batun yace “domin magance kokwanto, babu wannan daga Shugaban AfDB”
Hoton dake yawo a kafar sadarwa ta zamani, ɗauke da sanarwa cewa ya zaɓi Tinubu, wadda aka danganta ta da Tinubu, Oladokun yace ba gaskiya bane ba.
KARANTA WANNAN LABARIN: 2023: CBN ta ƙaryata rahoton Emefiele na neman takarar Shugaban Ƙasa
A cikin jawabin da aka ƙaryata da aka ce Adesina ya faɗa yace “idan Sanata Bola Tinubu zai iya mayar da Lagos jaha ta 5 dake da Tattalin Arziki a Afirka, to tabbas zaiyi haka ga Najeriya.”
Amma Oladokun ya karyata batun, yana mai cewa Adesina bai fitar da sanarwa makamanciyar haka.