Gamayyar Ƙungiyoyin Arewa sun koka na yadda Ƙungiyar Dattawan Inyamurai suka ajiye wani dabara nasu da sauran Ƙungiyoyi domin ganin Shugaban Ƙasa ya fito daga Yankin Kudu maso Gabas, yana cewa hanyar da suka ɗauka bata yi ba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Tunda Emefiele zaiyi Takara, Zamu Kwashe Mahimman Kayayyakin mu daga CBN — Inji INEC
Ƙungiyar ta kuma yi zargin cewa Shuwagabannin Inyamurai sune suke haifar da ƙalubale a Tsaron Kasa, da irin gargaɗin su data keyi cewa idan aka cire yankin Kudu maso Gabas a Shugabancin Ƙasa a Shekarar 2023, zai ruguje Najeriya, domin hakan ya saɓa ƙa’idar su.
Ƙungiyar ta kuma kira da ayi saurin kama Shugaban Ƙungiyar Tsohon Gwamnan Jahar Anambra Chief Chukwuemeka Ezeife daya gargaɗi ga Kasa da Al’ummar ta.
Mai Magana da Yawun Ƙungiyar Abdulazeez Suleiman ya bayyana haka a lokacin taron Manema Labaru a ranar Alhamis da daddare.
Yace kuma ƙalubalanci wasu Shugabannin Inyamurai, wanda Acewar sa abun kunya ne yankin ya fito da shugaban kasa na gaba domin ya lalata tsarin Shari’ar Ƙasar, ta hanyar matsawa ɓangaren Shari’a su saki Shugaban IPOB Mazi Nnamdi Kanu
Comments 1