Gabanin Babban taron jam’iyyar APC na kasa, Mai Tsawatarwa na majalisar dattawa, Orji Uzor Kalu, ya bukaci jam’iyyar ta tsayar da Dan Takarar shugaban kasa da yafito daga yankin kudu maso gabas.
Kalu ya ce muddin jam’iyyar ta amince da Mika tikitin takarar shugaban kasa ga yankin kudu, Toh ya kamata yankin kudu maso gabas ne zai Sami wannan damar.
Tsohon gwamnan jihar Abia ya bayyana haka ne yayin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai a Abuja ranar Talata, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran Kasa NAN ya ruwaito.
Dangane da burin Jigon jam’iyyar APC na kasa, Bola Tinubu, dan majalisar ya ce duk da cewa, Tunubu ya bayyana nashi aniyar, ba shi da wani abu da ya saba wa burin Tinubu, amma ya yi imanin cewa yankin kudu maso gabas suna bukatar Dan takarar shugaban kasa.
“Ban ga burin Tinubu yana da wani sabani ba ga Mai Neman shugabancin Najeriya daga yankin Igbo.
“Muna magana ne kan yadda Najeriya ta kasance, muna magana ne da ya kamata mutane su yi imani da shi.
“Babu wani dan kabilar Igbo tun bayan samun ‘yancin kai da aka zaba ta hanyar dimokradiyya a matsayin shugaban kasa,” in ji shi.