Dan takarar gwamna karkashin Jam’iyyar NNPP a jihar Gombe Alhaji Khamisu Ahmed Mailantarki, ya bayyana Mista Hamma Tanimu Abubakar a matsayin abokin takararsa wato wanda zai masa mataimaki a zaben 2023.
A wani sako da ya aikewa ‘yan jaridu, Mailantarki ya ce, ya kai ga yanke shawarar zabar Tanimu a matsayin wanda zai tsaya takarar mataimakin ne bayan tuntubar da ya dace, “Bayan tuntubar juna na yanke shawarar daukar Hamma Tanimu Abubakar a matsayin abokin takarata,” ya kara da cewa.
Malam Tanimu Hail daga Banganje da ke karamar hukumar Billiri a jihar Gombe, Abubakar ya halarci makarantar firamare ta Kashere da Kwalejin malamai ta Bauchi da kuma Advanced Teachers College da ke Azare.
Ya kuma taba zama Shugaban AC a shekarar 2007, Shugaban Karamar Hukumar Billiri kuma Mai Ba da Shawara ta Musamman kan Muhalli ga tsohon Gwamna Muhammadu Danjuma Goje.
(PRIMETIMENews)