2023: Ganduje yaƙi goyon bayan Takarar Amaechi ta Shugaban Ƙasa
Gwamnan Jahar Kano Abdullahi Umar Ganduje yaƙi goyon bayan tsohon Ministan Sufuri Rotimi Amaechi akan Takarar Shugaban Ƙasa a Shekarar 2023.
Amaechi ya ziyarci Kano a ranar Laraba a matsayin wani ɓangare na neman shawara, gabanin zaɓen fidda Gwani na shugaban Ƙasa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ƴan bindiga sun kashe mutane 4 a gidan Wani Ciyaman a Ebonyi
Tsohon Ministan ya ajiye mukaminsa daga cikin ƴan Majalisar Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari domin neman Takarar Shugaban Ƙasa a ƙarƙashin Jam’iyar APC.
A taro da masu ruwa da tsaki na ƴan Jam’iyyar APC, Ganduje yace Kano Jahar Kano ” Jaha ce mai canje-canje, kuma zata cigaba da haka”.
Ya ƙara dacewa Amaechi zai san inda Jahar ta dosa a lokacin da ya kamata.
Amaechi wanda ya bayyana cewa ƴan Jam’iyyar APC tuni suka san inda biyayyar Ganduje ta dosa, yace yazo Kano domin ya canja mashi ra’ayi cewa, yafi Kowane Ɗan Takara Cancanta.
Haka zalika, Amaechi ya ziyarci Gwamnan Jahar Lagos inda shima bai amince mashi ba, yana mai cewa Bola Tinubu shine Suka zaɓa.
Ganduje tuni aka san Makusancin Tinubu ne, dake neman Takarar Shugaban Ƙasa.