Gabanin zaben shekarar 2023, Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas na daukar kwararan matakai na ganin jihar ta kasance karkashin ikon sa.
Hakan ya biyo bayan nadin masu ba da shawara ga bangarori daban-daban na siyasa a jihar su 14,000.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Tarayya Ta Amincewa Gwamnan APC Ya Gina Kata Faren Filin Jirgin Sama A Jihar Sa
Ana iya kallon nadin a matsayin wani yunƙuri na yin iko da tsarin jam’iyyar a jihar.
Ku tuna cewa gwamna Wike da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, sun fafata a rikicin siyasar da ke neman shugabancin jam’iyyar.
Hakan ya fito ne a wata sanarwa dauke da sa hannun mai magana da yawun gwamnan, Kelvin Ebiri.
Ya ce masu ba da shawara za su taka rawar gani a harkokin mulkin jihar.
Sanarwar ta kara da cewa: “Baya ga nadin masu ba da shawara 14,000, Gwamna Wike ya kuma nada jami’an hulda da mazabu 319 da jami’an hulda da kananan hukumomi 40.”
“Nade-naden sun fara aiki nan take,” in ji shi.
A wani labarin kuma , Da Dumi-Dumi: Masarautar Ingila Ta Sanar Da Ranar Da Za Ayi Bikin Nadin Sarautar Sarki Charles III
Za a yi bikin nadin sarautar Sarki Charles III na Burtaniya a ranar Asabar, 6 ga watan Mayun shekarar 2023 dake tafe.
Za a yi bikin ne a Westminster Abbey, in ji fadar Buckingham.