Gwamnatin tarayya ta amince da gina filin jirgin saman Lekki a yankin Lekki-Epe dake jihar Legas.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa gwamnatin jihar Legas ta ce za ta fara aikin gina sabon filin jirgin sama a yankin Lekki-Epe na jihar a shekarar 2023 dake tafe.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Dumi-Dumi: Masarautar Ingila Ta Sanar Da Ranar Da Za Ayi Bikin Nadin Sarautar Sarki Charles III
Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika ne ya mikawa Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu amincewar gina sabon filin jirgin a madadin gwamnatin tarayya a taron tattalin arzikin Legas na 2022 da aka gudanar a Eko Hotel da Suites dake Legas.
Babban mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Legas kan sabbin kafafen yada labarai, Jubril Gawat, ya bayyana hakan a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Gawat ya rubuta cewa, “Gwamnan jihar Legas, @jidesanwoolu ya karbi amincewar gwamnatin tarayya a hukumance na gina filin jirgin saman Lekki Epe a yau a taron tattalin arzikin Legas, Ehingbeti 2022 a Otal din Eko da Suites.”
“Hon.Ministan Sufurin Jiragen Sama, @hadisirika ya bayyana mahimmancin filin jirgin saman Lekki-Epe. Ya ce Legas na da matukar muhimmanci ga tattalin arzikin kasar, kuma filin jirgin na Murtala Muhammed na yanzu ya cika cunkoso.”
“Gwamnan jihar Legas, ya ce akwai sauran labarai masu kyau da za su zo a taron tattalin arzikin Legas na Ehingbeti 2022 kuma ‘yan Legas su sa ido.”
Da yake gabatar da amincewa ga Sanwo-Olu, Sirika ya ce, “Da ikon Allah mafi rahma, mu a ma’aikatar sufurin jiragen sama mun yi farin cikin bayar da wannan amincewa ga jihar Legas. Ya zama abin hangen nesa ga Legas, ga jama’arta, makomarta, arzikinta, kasa, da kuma bil’adama.”
A wani labarin kuma, Kasar Amurka Ta Dawowa Da Najeriya Tagulla 23 Da Aka Wawure
Kasar Amurka ta dawowa da Najeriya Tagulla 23, daga cikin dubunnan kayayyakin tarihi da turawan mulkin mulaka’u na Ingila suka wawashe a lokacin da suka mamaye masarautar Benin a shekarar 1897.
A wajen bikin dawo da Tagullar da aka yi a birnin Washington, DC ranar Talata, Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed ya yabawa Amurka kan mayar da kayayyakin tarihi da aka sace.