2023: Gwamnan Bauchi ya buƙaci masu maƙamai dasu ajiye muƙaman su idan har zasu yi takara
Gwamnan Jahar Bauchi Bala Mohammed ya baiwa masu riƙe da muƙaman siyasa da Ma’aikata a Gwamnatin sa kwanaki biyu, domin su ajiye, idan har suna Son yin takarar duk wats Kujerar Siyasa a Babban Zaben Shekarar 2023.
Mai baiwa Gwamnan Shawara na Musamman akan Kafafen Yaɗa Labaru Mukhtar Gidado ya bayyana haka a cikin wata sanarwa daya aikewa ƴan jarida a Jahar a ranar Laraba da daddare.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wani Mutumen Kenya ya kashe Matar shi, yaran sa 3, ya miƙa kashi ga Ƴan Sanda
Yace umarnin Gwamnan yana ƙunshe cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jahar Bauchi Ibrahim Kashim ya fitar.
Gidado yace “Sanata Bala Abdulkadir Mohammed (Kauran Bauchi) Gwamnan Jahar Bauchi ya umarci dukkanin masu riƙe da maƙaman Siyasa da Ma’aikata a Gwamnatin Jahar Bauchi da suke Son yin takara a Babban Zaɓe mai zuwa da su kawo takardar ajiye aikinsu ga Sakataren Gwamnatin Jahar zuwa ko kafin ranar Juma’a 18 ga watan Afrilu na Shekarar 2022.
“Wannan umarnin ya biyo bin Dokar zaɓe ta shekarar 2022 wanda ya bada umarnin cewa Masu riƙe da maƙaman Siyasa da sauran ƴan siyasa dake son yin takara a Babban Zaɓe na Shekarar 2023 dasu ajiye muƙami kafin kwanaki 30 a gudanar da zaben fidda Gwani a kujerar da suke nema.
“Umarnin na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jahar Bauchi ya fitar.
Comments 1