Tsohon Jigon jam’iyyar APC a jihar Zamfara, Sanata Kabiru Marafa ya bayyana dalilansa na ficewa daga jam’iyyar zuwa jam’iyyar PDP.
Jaridar Dimokuradiyya a baya ta ruwaito cewa tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, Sanata Kabiru Garba Mafara da magoya bayansu sun fice daga jam’iyyar APC inda nan take suka sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP a ranar Lahadi.
A cewar Marafa, jam’iyya mai mulki ta kasa ba gida ce a gare shi ba.
Ya ce jam’iyyar ta dauke shi a matsayin wanda aka yi watsi da shi da kuma yimasa rashin adalci a gare shi da dimbin magoya bayansa.
Tsohon dan majalisar tarayya ya ci gaba da bayanin cewa hatta a cikin tsohuwar jam’iyyarsa, wasu sun yi ta gwagwarmaya don ganin sun yi takaicin ficewa daga jam’iyyar da suka sha wahala wajen ginawa donmin raya kasa.
Ya ce sabon shugaban jam’iyyar na kasa Sanata Abdulahi Adamu ba zai yi wani abu daban da abin da tsohon shugaban riko na jam’iyyar Mai Mala Buni ya yi ba.
“Siyasa ita ce cin zabe da komai, don haka ba za mu iya zama a gidan da ba a bukatar mu,” in ji Marafa.
“A matsayina na, ni cikakken mutum ne mai dangane da wannan aik na jam’iyari APC. Idan har akwai abin da ya rage, ina jira in ga yadda maginin wannan zalunci ya yi wa al’ummar Jihar Zamfara, yadda za su kasance a siyasance.
“Amma a yanzu na ji dadi, na shaida musu a gaban su a Kaduna cewa ba za su taba cin gajiyar makircin da suke yi a wannan lokaci ba, wato Mai Mala da abokan tafiyarsa. Kuma na yi farin ciki cewa sun yi rashin nasara kuma sun ji kunya.
“APC ba Musulunci ba ce, addinina ne ba zan iya barin ba ta kowane dalili, amma jam’iyyar siyasa zan iya barin na shiga duk wanda na ga dama,” inji shi.