Wani mamba a jam’iyyar APC, Olumide Ajiboye ya ce dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a 2023, Bola Tinubu shi ne ya fi cancantar fitar da Najeriya daga durkushewar tattalin arzikin da take ciki.
Ajiboye, wanda memba ne na Kwamitin Yada Labarai a Majalisar yakin neman zaben Tinubu da Shettima ya yi magana a ranar Litinin din nan a matsayin bako a gidan Talabijin na Channels cikin shirin Sunrise Daily.
Dan jam’iyyar APC na mayar da martani ne kan rahoton da hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta fitar a makon da ya gabata na cewa ‘yan Najeriya miliyan 130 ke cikin matsanancin talauci, wanda ke wakiltar kashi 63 cikin 100 na al’ummar kasar.
KU KARANTA KUMA Tinubu Ya Yi Alkawarin Cika Duk Alkawuransa Da yi A Kamfen
Tuni dai jam’iyyun adawa suka yi kaca-kaca da gwamnatin APC ta Shugaba Muhammadu Buhari kan yadda ta jefa ‘yan Najeriya cikin talauci, sabanin alkawarin da ta yi a yakin neman zaben 2015 na cewa jam’iyyar za ta fitar da ‘yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci.
Sai dai Ajiboye a ranar Litinin nan ya ce Tinubu na da abin da zai iya fitar da Najeriya daga durkushewar tattalin arzikinta.
“Dan takararmu, Bola Ahmed Tinubu ya kware a fannin tattalin arzikin jihar Legas, wadda har yanzu ita ce mafi karfin tattalin arziki a Najeriya, kuma a tsawon lokaci, shi ya sa nake ganin watakila shi ne ya fi cancantar fitar da mu daga wannan rugujewar. ” in ji shi.
Dan jam’iyyar ta APC ya caccaki jam’iyyar PDP, inda ya ce jam’iyyar ta shafe shekaru 16 tana mulki tsakanin 1999 zuwa 2015 amma “ko da yaushe ta ki amincewa da karya arzikin Najeriya wanda ya sa ‘yan Najeriya suka kada kuri’a a APC a 2015”.
Ajiboye ya bukaci ‘yan Najeriya da kada su mayar da hankali sosai kan “masu jan hankalinsu” amma su mai da hankali kan batutuwan da za su ceto Najeriya.
Manyan masu kalubalantar Tinubu sun hada da Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP da Peter Obi na jam’iyyar Labour a fafatawar da aka bayyana a matsayin tseren doki uku.
A Wani Labarin Kuma Buni Ya Kaddamar Da Tsarin Shirin Raya Kasa na Shekara 10 A Damaturu
Gwamna Mai Mala Buni na Yobe ya kaddamar da tsarin aiwatar da shirin raya kasa na shekaru 10 a Damaturu babban birnin jihar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Alhaji Usman Geidam, Kakakin Sashen Yada Labarai na Yobe (YOGIS) ya fitar a Damaturu ranar Lahadi.