Tsohon gwamnan jihar Legas kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Tinubu yana kasar Ingila tare da mukarrabansa.
A matsayin wani bangare na shirye-shiryen zaben 2023, ana sa ran Tinubu zai yi jawabi a zauren Chatham House, da ke Landan, kan ‘Renewed Hope Agenda’ wato Ajandar sabunta fatan da yake da shi a ranar Litinin din nan.
KU KARANTA KUMA Tinubu Ya Fadawa Kiristoci Dalilin Zabar Shattima A Mataimakinsa
DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa Dan takarar na jam’iyyar APC zai yi karin haske kan tsare-tsarensa na tsaro, tattalin arziki da kuma manufofin kasashen waje a cibiyar nazarin harkokin ketare da manufofinta na Burtaniya nan da ‘yan sa’o’i masu zuwa.
Ya samu rakiyar kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, gwamnonin jihohin Jigawa da Kaduna, Abubakar Badaru, Nasir El-Rufai da kuma tsohon gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi.
Asiwaju ya bayyana a cikin takardarsa na nuni da aniyar kafa wata kyakkyawar manufa da za ta iya samar da ingantaccen tsarin manufofi don magance ta’addanci da fashi da makami da garkuwa da mutane da sauran nau’o’in miyagun ayyuka da ke haddasa barna a kasar nan.
A Wani Labarin Kuma Yadda Na Zama Mataimkain Dan Takarar Shugaban Kasa – Bishop Idahosa
Mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Bishop Isaac Idahosa, a ranar Litinin, ya bayyana yadda dan takarar jam’iyyar, Rabiu Kwankwaso ya zabe shi a matsayin mataimakinsa.
Idahosa, wanda ya yi magana kai tsaye a gidan talabijin na Channels a shirin Sunrise Daily, ya ce ba shi da wani buri na tsayawa takara a siyasance a lokacin da aka bayyana shi a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa na NNPP a watan Yuli.