Jigon Jam’iyyar APC Bola Tinubu ya bar Najeriya, Makonni kaɗan bayan ya bayyana aniyar sa na tsayawa takarar Shugaban Ƙasa a shekarar 2023, kamar yadda Jaridar The PUNCH.
Wani mamba dake aiki da Kwamitin takarar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya shaidawa majiyar mu a ranar Juma’a, cewa tsohon Gwamnan Jahar Lagos ya tafi ƙasar waje domin yin tsare-tsare da hutawa.
KARANTA WANNAN LABARIN: An Yanke Wa Wasu Masu Damfara Ta Yanar Gizo Shida Hukuncin Zaman Gidan Kaso A Osun-Ekiti
Majiyar wanda ya buƙaci a sakaya Sunan sa yace “Tinubu ya tafi ƙasar waje bayan ya zagawa ƙasar domin neman shawarwari. Ya tafi domin ya shirya tsare-tsare da hutawa.”
Majiyar bata bayyana ƙasar da Tinubu ya tafi ba. Yace ba gaskiya bane ace Jigon Jam’iyyar ya tafi neman lafiya.
Duk wani ƙoƙari da aka yi domin jin tabakin Mai Magana da Yawun Tinubu Tunde Rahman bai samu ba a ranar Juma’a, kuma bai maido da saƙon da aka tura masa ba.
Haka zalika, duk wani ƙoƙari najin tabakin Darkta-Janar na Ƙungiyar Tinubu Support Group, Abdulmumin Jibrin shima bai samu ba.