By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, ya roki gwamnatin tarayya da ta karbe ragamar kula da jami’ar kimiyyar likitanci da kuma asibitin koyarwa na jami’ar da ke jihar domin basu kulawa da kyau.
Umahi ya yi wannan kira ne ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a ziyarar aiki ta kwanaki 2 da ya kai jihar.
Kebbi: Malami Ya Fi Sauran ‘Yan Takara Yin Fice – Matawalle
Gwamnan wanda ya jagoranci Muhammadu Buhari zuwa Jami’ar Kimiyyar Likitanci ta Jihar ya ce ya kamata gwamnatin tarayya ta karbe asibitin koyarwa na jami’ar domin ya fi karfin kowace jiha ta sarrafa.
Ya ce, “Tun da farko na roki shugaban kasa ya amince da karbe mulkin asibitin kuma ya ce mu je mu yi biki, kuma tun a wancan lokacin muke ta biki.
Gwamnan ya ce asibitin zai magance kalubalen da yawon bude ido da likitoci ke fuskanta a kasar saboda yana da ingantattun kayan aiki da ake iya samu a ko’ina a duniya.
Da yake mayar da martani, shugaban kasa Muhammadu Buhari yayin kaddamar da ayyukan ya yabawa gwamnan kan yadda ayyukan suka kasance masu inganci.
“Buhari ya lura cewa ya gamsu da ayyukan gwamnan, tare da lura cewa aikin yana kama da wanda zai dore” ya kara da cewa.