Babban Sufeto Janar na ‘yan sanda, Usman Baba, ya bukaci jami’an ‘yan sanda da su tabbatar da an dakatar da kona ofisoshin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC cikin gaggawa.
Mista Baba ya ba da wannan umarni ne a ranar Juma’ar nan a Abakaliki yayin da yake jawabi ga jami’an rundunar a wani bangare na gudanar da ziyarar aiki da ya kai jihar.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Babban sufetan ya bukaci ma’aikatan da su yi duk mai yiwuwa wajen kare kayayyakin INEC da sauran kayayyakin jama’a a jihar.
KARANTA KUMA IGP Zai Gana Da Jam’iyyun Siyasa Da ‘Yan Takararsu
“Hanyoyin harin da wadannan ‘yan bindigar ke kai wa suna da sarkakiya saboda suna jefa bama-bamai da abubuwa masu hadari da sauransu daga nesa.
“Mun yi imanin cewa baya ga samar da tsaro na zahiri a ofisoshin INEC, ya kamata ku hada kai da jami’anta wajen samar da ofisoshi ga ma’aikatanmu,” in ji shi.
Alkali Baba ya ce babban nauyi ne da ya rataya a wuyan ‘yan sanda su samar da tsaro a ofisoshin INEC da ke fadin jihar tun kafin da kuma bayan zabukan da ke tafe.
“Ya kamata a mayar da ofisoshin INEC da ke a fadin jihar zuwa wurare masu tsaro idan zai yiwu amma idan ba haka ba, sai a mayar da muhimman kayayyaki zuwa wurare masu tsaro.
“Na yaba da duk kokarin da kuke na kare rayuka da dukiyoyi a Ebonyi da irin taimakon da gwamnatin jihar ke baiwa rundunar,” in ji shi.
Ya kuma lura cewa ayyukan hukumar tsaro ta Ebubeagu a jihar ya kamata ‘yan sanda su kula da su domin bai kamata su rika gudanar da ayyukansu ba tare da tantancewa ba.
A Wani Labarin Kuma Shari’ar Kisan Ummit: Kotu Ta Kira Jami’in Lafiya, Mahaifiyarta Da Dan Sanda
Wata babbar kotun Kano a ranar Juma’ar nan ta umarci gwamnatin jihar Kano da ta dawo da mahaifiyar Ummulkulsum, Fatima Zubairu da PC Aminu Halilu domin yi musu tambayoyi kan zargin kisan da ake yiwa wani dan kasar China, Frank Geng-Quangrong, mai shekaru 47.
Ana tuhumar Mista Frank, wanda ke zaune a Railway Quarters Kano da laifin kisan kai, kuma ya aikata laifin ne a ranar 16 ga watan Satumba, a Janbulo Quarters Karamar Hukumar Gwale da ke Kano.