Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya ce zai kayar da abokan hamayyarsa a zaben 2023 kamar yadda Arsenal ta yi nasara a kan Chelsea a gasar Premier ta Ingila.
Arsenal ta koma saman teburin gasar Premier bayan da ta doke Chelsea da ci 1-0 a Stamford Bridge a ranar Lahadi.
KARANTA ANAN: Yadda Dan Shekarun 32 ya Angwance da mata 3 Rigis lokaci daga
Wannan nasara na zuwa ne bayan da Gabriel Magalhaes ya ci kwallon.
Yayin da yake taya Gunners murna, tsohon mataimakin shugaban kasar, wanda kuma mai goyon bayan Arsenal ne, ya yi alkawarin yin haka ga ‘yan Najeriya a zaben shugaban kasa na watan Fabrairun 2023.
Ya rubuta a shafin sa na Twitter cewa, “Babban nasara, Arsenal, ko da bayan an tashi wasan babu ci.
”Kamar yadda Arsenal ta yi a wannan wasa domin mu magoya baya, mu ma za mu mai da Najeriya ga ‘yan Najeriya.”
A wani labarin kuma: Magoya Bayan PDP da yawa sun koma APC a Sokoto
Wasu ‘ya’yan jam’iyyar PDP sun sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC), a jihar Sokoto.
Shugaban jam’iyyar APC a jihar wanda ya karbi masu sauya shekar a ranar Lahadin da ta gabata, ya ce sauya shekar da suka yi rage karfi ne ga jam’iyyar PDP daga gundumomin Dundaye, Gumburawa da Gidan Bubu a karamar hukumar Wamakko.
Ministan harkokin ‘yan sanda, Maigari Dingyadi, wanda ya yi jawabi a wajen taron, ya bayyana ci gaban da aka samu a matsayin nasara.