2023: Zan Iya Yanka Ɗan Yatsa Na Don Dangwalawa Uba sani Ƙuri’ar zama Gwamnan Kaduna – Inji Matashiya Zainab
Wata Matashiya ƴar Jihar Kaduna mai suna Zainab Abubakar Bako tasha alwashin zaɓar Sanata Uba sani a matsayin Gwamnan jihar kaduna, ko da kuwa za ta yi amfani da jininta ne amatsayin tawadar dangwala wa Sanatan.
Zainab ta rubuta haka ne a shafinta na Facebook, tana mai cewa ita a halin yanzu kallon Gwamnan Jahar Kaduna take yiwa Malam Uba Sani ba wai Sanata ba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan Bindiga Sun Ƙaddamar da Munanan Hare-hare a Ƙananan Hukumomi 3 Na Jihar Katsina
Matashiyar Yar A Mutum Sanatan ta rubuta kamar haka “Kallon Gwamna nake yiwa Sanata Uba Sani bawai Ɗan Takarar Gwamna ba, Dan mu Lokacin rantsarwa kawai muke Jira da Ikon Allah”.
“Nayi Alƙawarin zan zaɓi Uba Sani, da kuɗi na, da lokaci na, da kuma Basirar da Allah ya bani, sannan zan shiga lungu da saƙo na Ƙaramar Hukuma ta, da Gunduma a, da kuma Mazaɓa ta, domin neman goyon baya, tare da wayar wa Iyaye Mata da Matasa kai dan su zaɓi Ɗan Takara a matsayin Gwamnan Sanata Uba Sani”. Inji Sanata.
A cewar ta, duk cikin Ƴan Takarar Gwamnan da muke dasu a Jahar Kaduna babu wanda ya kai Sanata Uba Sani cancanta da kawo wa Jahar Kaduna cigaba ta fannoni daban-daban na rayuwa.
Zainab ta bayyana cewar Malam Uba Sani ya yi an gani kuma an shaida, babu wani Sanata a fadin Najeriya da ya taɓa kai ƙudiri 21 irin sa.
“Jihar Kaduna na buƙatar Shugaba jajirtacce mai shiga sahun gaba akan dukkan damuwan Talakawan sa, kuma Ɗan Siyasar da yasan Darajar Al’ummar da yake Wakilta irin Sanata Uba Sani.
Ina sake kira ga Al’ummar Jahar Kaduna, Iyaye, Maza, da mata da Matasa, ku fito mubi Jirgin tsira, domin kai mu tudun mun tsira,
Mu tanada, mu Ajiye, kuma muyi tattalin Katukan Zaɓen mu, domin dangwalawa Hon. Uba Sani ƙuri’a a zaɓen Shekarar dubu biyu da Ashirin da Uku, Allah ka bamu nasara.
Malam Uba Sani shine zaɓi na kuma zabin Al’umar Jahar Kaduna da yardan Allah.
Sanata Uba sani shine Dan takarar Gwamnan jihar kaduna ƙarƙashin jam’iyar APC mai Mulki.