Hedikwatar tsaro ta bayyana cewa sojojin Nijeriya sun kawar da ‘yan ta’adda 6,880 da sauran masu laifi tare da kama wasu 6,970 daga watan Janairu zuwa yau.
Darakta mai kula da ayyukan yada labarai na tsaro, Maj.-Gen. Edward Buba ya bayyana hakan ne yayin da yake bayar da karin haske kan ayyukan rundunar a shekarar 2023, ranar Juma’a a Abuja.
Karanta nanMun Shirya Tsaf Domin Dawo Da Zaman Lafiya A Kudu Maso Gabascin Nijeriya-Tinubu
Buba ya ce sojojin sun kuma ceto mutane 4,488 da aka yi garkuwa da su tare da kwato makamai iri-iri har 3,320 da alburusai iri-iri 39,075 a cikin shekarar.
A cewarsa, sojojin sun kwato lita miliyan 100.3 na danyen mai, lita miliyan 60.3 na AGO, lita miliyan 3.4 na DPK da kuma lita miliyan 3.5 na PMS a cikin shekarar.
A yankin Arewa maso Gabas, Buba ya kara da cewa dakarun Operation Hadin Kai sun yi nasarar kashe ‘yan ta’adda 1,759, sun kama mutane 953 tare da ceto mutane 826 da aka yi garkuwa da su, yayin da ‘yan ta’addan BH/ISWAP 11,015 da iyalansu suka mika wuya.
Kakakin rundunar ya ce an kwato bindigogi kirar AK47 guda 259, bindigogin FN na ma’adana 681, harsasai 7,097 na ammo na musamman 7.62mm, 5,773 na 7.62mm NATO, 495,336 alburusai iri-iri da kuma dabbobi 2,059.
A yankin Arewa maso Yamma, ya ce dakarun Operation Hadarin Daji sun kashe ‘yan ta’adda 1,522, sun kama mutane 645 da ake zargi da kuma kubutar da mutane 1,101 da aka yi garkuwa da su.
A wani labarin kumaGwamna Adeiyatiwa Na Jahar Ondo Ya Saka Hannu Akan Kasafin Kudin Jahar
Kayayyakin da aka kwato a cewarsa sun hada da bindigogi kirar AK47 guda 53, makamai iri-iri 426, alburusai 2,342 na musamman 7.62mm, alburusai iri-iri 6,900 da kuma dabbobi 5,084.
Buba ya kara da cewa dakarun Operation Whirl Punch da ke yankin Arewa maso Yamma sun kuma kashe ‘yan ta’adda 992, sun kuma kama mutane 345 da ake zargi da kuma kubutar da mutane 538 da aka yi garkuwa da su a cikin shekarar.
Ya ce sojojin sun kuma kwato bindigogi kirar AK47 guda 34, makamai iri-iri 346, alburusai 4,792 na musamman 7.62mm, alburusai iri-iri 5,127 da kuma dabbobi 830.