Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun na Ogun, a ranar Juma’a, ya sanya hannu kan kasafin kudin shekarar 2024 na Naira biliyan 703.02.
Gwamnan yayin da ya ke rattaba hannu kan kudirin dokar ya ce kasafin zai kara habaka ci gaban jihar tare da mayar da ita cibiyar samar da ababen more rayuwa a Najeriya.
Karanta nan2023:Sojoji Sun Kashe Yan Ta’adda 6,880 Cikin Shekara 1-Hedikwatar Tsaro
Gwamnan ya yi magana ne a ofishinsa da ke Abeokuta bayan ya sanya hannu kan kudirin dokar da Mista Olakunle Oluomo, kakakin majalisar dokokin Ogun ya gabatar masa.
Kasafin kudin mai taken “Budget of Sustained Growth and Development,” an gabatar da shi ga majalisar a ranar 30 ga Nuwamba, ta hanyar gwamna.
A cewar gwamnan, jihar ta ci gaba da samun bunkasuwa a cikin shekaru biyar da suka gabata, inda ya bayyana cewa kasafin kudin ya shaida yadda gwamnatinsa ta himmatu wajen aiwatar da manufofinta.
Lokacin da muka shiga ofis a ranar 29 ga Mayu, 2019, mun himmatu wajen ganin mun samar da yanayin da zai taimaka wajen saka hannun jari da masu zuba jari a jihar Ogun.
Mun yi imanin cewa yana da matukar muhimmanci ga ci gaban tattalin arzikin jiharmu da kuma ci gaban daidaikun jama’armu.
A wani labarin kumaGwamna Adeiyatiwa Na Jahar Ondo Ya Saka Hannu Akan Kasafin Kudin Jahar
A yau, muna da kasafin kudin da ya zama doka, wanda ya ninka kasafin kudinmu sau biyu a lokacin da muka karbi mulki.
Shekaru zuwa shekara, mun samu nasarar aiwatar da kasafin kudinmu zuwa mafi karancin kashi 70 cikin 100,” in ji shi.
Jahar Ogun dai a yan lokutan nan ta zama wata matattarar zuba jari daga yan kasashen waje dama na kasa Nijeriya,abinda ya janyo jahar take samun bunkasar kasuwanci da kaso 60 cikin 100 a cikin shekaru uku kacal.