Uwargidan gwamnan jihar Borno, Dakta Falmata Babagana, ta bukaci shugabannin addini da na al’umma da su tallafawa mata wajen samun cibiyoyin kiwon lafiya saboda ta’azzarar matsalar haihuwar jarirai a gida a jihar.
Ta yi magana ne a lokacin da take kaddamar da gangamin wayar da kai na makon shayarwa ta duniya na bana mai taken, “Mu tashi tsaye domin shayar da nono uwa,” a Maiduguri ranar Talatar nan.
KARANTA WANNAN: https://dimokuradiyya.com.ng/wata-babbar-kotu-ta-raba-auren-shekara-23-da-aka-yi-tsakanin-wani-mutum-da-jikarsa/
Ta ce an gudanar da gangamin ne domin dakile dabi’ar haihuwar jarirai a gida a jihar.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Uwargidan gwamnan, wacce kwamishiniyar harkokin mata, Zuwaira Gambo ta wakilta, ta ce wannan dabi’a na hana mata damar samun ilimi, ba da shawara da kuma tallafawa kwararrun kiwon lafiya.
“Yayin da ake rage yawan adadin haihuwa a gida, iyaye mata da jarirai suna bukatar tallafi da kulawa daga dangi don farawa da ci gaba da shayar da jarirai. Bugu da kari, suna bukatar tallafi daga shugabannin addini da na al’umma, tsarin kiwon lafiya, wuraren aiki da gwamnati don shayar da nonon uwa har tsawon lokacin da ake so,” inji ta.
A wajen taron, Shugaban Asusun Tallafawa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) na ofishin yankin Maiduguri, Samuel Sesay, ya ce shayar da jarirai nonon uwa zalla na taka muhimmiyar rawa wajen shawo kan matsalar rashin abinci mai gina jiki, tare da taimakawa yara su samu lafiya.
Jami’ar kula da abinci da motsa jiki ta Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) Dokta Pindal Wakawa, ta jaddada bukatar samar da ilimi da dokoki domin kariya da tallafawa yara.