Shugaban Jam’iyyar APC na Jahar Bayelsa Dr Dennis Otiotio yace tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan yana da damar da zai shigo Jam’iyyar, amma har yanzu yaƙi yi.
Otiotio ya bayyana haka ga Kamfanin Dillancin Labaru na Ƙasa a tattaunawar sa ta waya a ranar Talata.
Ya yi jawabi akan yunƙurin maido dashi daga cikin masu neman takarar shugaban ƙasa a Shekarar 2023, yana mai cewa APC a Bayelsa batasan da zaman shi cikakken Ɗan Jam’iyya ba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Matasa Sun Zama Saniyar Ware Saboda Tsadar Fom Din Takarar Da APC Da PDP Suka Sanya — Yiaga Africa
“Har Yanzu tsohon Shugaban Ƙasa bai yi Rajistar zaman sa ɗan Jam’iyya ba. Yana da damar da zai shiga kowacce Jam’iyya dayake muradi.
“Ƙofar mu a buɗe take mu karɓe shi, a matsayin mu na Jam’iyyar dake Son cinye zaɓe, hanya kaɗai da zamu iya yin haka, shine ta hanyar amsar mutane zuwa Jam’iyyar,” inji Otiotio.
Wata Ƙungiya mai goyon bayan shi a ranar Litinin a Abuja ta sayi Tikitin Tsayawa Takarar Shugaban Ƙasa a Babban Zaɓe na Shekarar 2023 a ƙarƙashin Jam’iyar APC.
Amma a sanarwar da mai Taimakawa Jonathan yayi akan Kafafen Yaɗa Labaru Ikechukwu Eze a daren ranar Litinin yace Tsohon Shugaban Ƙasa ya nisanta kanshi da wannan Tikiti, yana mai cewa bai sanya kowa ya siya mashi Tikiti ba.
A cewar sanarwar ba’a tuntuɓi Jonathan kafin a siya mashi Tikitin Tsayawa Takarar Shugaban, a saboda haka baya so.