Gabanin babban zaben shugaban kasa da za a yi a watan Fabrairun 2023, gwamnoni biyar da aka zaba a karkashin jam’iyyar PDP a ranar Lahadi sun gana a jihar Enugu.
Majiyar cikin gida ta shaidawa Jaridar DAILY POST cewa tattaunawar ta ta’allaka ne kan yadda za a kai dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Mista Peter Obi a 2023.
DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa, Gwamnonin sun hada da: Samuel Ortom na jihar Benue, Nyesom Wike na jihar Ribas, Seyi Makinde na jihar Oyo, Okezie Ikeazu na jihar Abia da kuma mai masaukin baki gwamnan jihar Enugu, Ifeanyi Ugwuanyi.
KARANTA KUMA: Wasu Jiga-jigan PDP Sun Roki Wike Da A Sulhunta Kafin Babban Zaben 2023
A cewar majiyar, gwamnoni biyar sun koma bayan tazarcen Peter Obi ne saboda basu gamsu da dan takarar PDP Atiku Abubakar ba.
Jaridar DAILY POST ta ruwaito cewa matakin da gwamnonin suka dauka ba zai iya rasa nasaba da rikicin da ya dabaibaye babbar jam’iyyar adawar.
Rikicin wanda ya samo asali ne sakamakon arangamar da aka yi tsakanin Wike da tsohon mataimakin shugaban kasar, duk da kokarin da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar ke yi na dakile rikicin.
A wani labarin kuma: ‘Yancin Kai: ‘Yan Najeriya Sun Rufe Titin New York Yayin Da Suke Tattaki
‘Yan Najeriya daga sassa daban-daban na kasar a ranar Asabar din nan sun sanya wa birnin New York fentin fari da kore.
Kamfanin dillancin Labarai Kasa NAN ya ruwaito cewa shugabannin al’ummar Najeriya da wakilai sun bi sahun sauran ‘yan kasar domin rufe wasu sassan titin Second Avenue na Midtown na wani dan lokaci.