Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya musanta janyewa daga takarar shugaban Kasa.
Tinubu ya saka wani dan gajeren hoton bidiyonsa a kan wani shafi a yammacin ranar Lahadin nan, a wani yunkuri na karyata jita-jitar da ake yadawa.
DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa, Tsohon Gwamnan Jihar Legas ya rubuta tare da cewa: “Da yawa sun ce na mutu; wasu kuma na cewa na janye daga yakin neman zaben shugaban kasa.
“Lafiyata kalau…… ina da karfi.
KARANTA KUMA: Wata Baraka Na Neman Kunno Kai Tsakanin Tinubu Da Wasu Jiga-jigan APC
“Wannan ita ce gaskiyar: Ina da ƙarfi, ina cikin koshin lafiya kuma a shirye nake in bauta wa ‘yan Najeriya tun daga rana ta ɗaya.”
Tinubu ya fuskanci suka yayin da ya bace a rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a ranar Alhamis din da ta gabata.
Yarjejeniyar zaman lafiya takarda ce da ‘yan takarar shugaban kasa suka sanya wa hannu gabanin babban zaben kasar.
Jaridar Daily Post ta rawaito cewa, Sai dai Tinubu ya samu wakilcin mataimakinsa,
Kashim Shettima, wanda tsohon gwamnan jihar Borno ne a wajen taron.
Manyan ‘yan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP, Peter Obi na jam’iyyar Labour Party (LP), Rabiu Kwankwaso na jam’iyyar NNPP duk sun hallara.
A wani labarin kuma: 2023: Wike, Ortom, Da Wasu Gwamnoni Sun Hadu A Enugu Kan Peter Obi
Gabanin babban zaben shugaban kasa da za a yi a watan Fabrairun 2023, gwamnoni biyar da aka zaba a karkashin jam’iyyar PDP a ranar Lahadi sun gana a jihar Enugu.
Majiyar cikin gida ta shaidawa Jaridar DAILY POST cewa tattaunawar ta ta’allaka ne kan yadda za a kai dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Mista Peter Obi a 2023.