Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mayar da martani kan dalilin da ya sa yaran kasar da ba sa zuwa makaranta ke karuwa.
Adadin yaran da ba sa zuwa makaranta a Najeriya ya kai miliyan 20 bisa ga kididdigar da hukumar kula da ilimi, kimiya da al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO ta fitar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zan Magance Rashin Tsaro Tare Da ‘Yan Banga Da Mafarauta – Zababben Gwamna
Alkaluman sun nuna cewa Indiya, Najeriya da Pakistan ne suka fi yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a duniya a tsakanin shekaru 6 zuwa 18.
A cikin hirar da gidan Talabijin na Channels ta yi wanda DAILY POST ta sanyawa ido, mai ba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara ta musamman kan harkokin zuba jari, Maryam Uwais, ta zargi al’ummar kasar da karuwar yaran da ba sa zuwa makaranta.
Ta bayyana cewa wasu yara ba sa zuwa makaranta a Arewacin Najeriya saboda biyan harajin N80.
Uwais ta dage cewa dole ne gwamnatocin jihohi su tashi tsaye wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta.
“Muna da yawan jama’a da ke karuwa da sauri fiye da tattalin arzikinmu, kuma ba mu yi niyya ga waɗannan batutuwan da ke kara yawan adadin ba. Akwai bambance-bambance da yawa. Muna buƙatar sanin dalilin waɗannan lambobin. Muna bukatar mu kasance masu dabara ta hanyoyin magance matsalar.
Don haka yana da mahimmanci a sanya ido kan lamarin, don samun abin da ya haifar da ba da amsa a matsayin martani. Muna karkashin Hukumar Kididdiga ta Kasa; za su iya nazarin abubuwan da ke faruwa kuma su magance batun.
“Zan ba ku misali; Ina wata jiha, ba zan gaya muku jiha ba, amma jihar arewa ce, na ga yara 13 suna wasa, sai na tambaye su, ‘Me ya sa ba kwa zuwa makaranta? Sun ba da abubuwa daban-daban, kuma dukansu suna da buri tun suna yara ƙanana. Sun ce ba sa makaranta saboda Naira 80 a matsayin harajin iyaye ko wani abu makamancin haka.
“Yanzu, idan za mu iya amfani da irin wadannan bayanan da ke fitowa daga dukkan al’ummomi ko kuma kasancewar matsalar da ta fi kamari ga yaran da ba su zuwa makaranta, za a iya magance shi a matakin gwamnatin jiha domin wadannan wasu faya-fayen haraji ne da ke tasiri ga damar zuwa makaranta. .” Inji ta.
A wani labarin kuma, Gwamnatin Kano Zata Ba Da Hutun Makarantu Saboda Zuwan Watan Azumi
Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano, a ranar Alhamis, ta amince da ranar 7 ga watan Afrilu, 2023, a matsayin ranar da za a fara hutun zango karatu na biyu/Ramadan ga dukkan makarantun gwamnati na furamare, sakandire na jeka ka dawo da na kwana da masu zaman kansu a fadin jihar.
Gwamnati ta bukaci iyaye da masu kula da daliban makarantun kwana da su kwashe ‘ya’yan su zuwa gida da sanyin safiyar Juma’a (gobe).