- Gwamnatin tarayya ta sauya sunan ma’aikatar sufurin jiragen sama zuwa ma’aikatar sufurin jiragen sama da na sararin samaniya.
- Zirga-zirgar jiragen sama da sararin samaniya suna da alaka da juna.
- Najeriya na da bukatar ta fito da manufofinta don daidaitawa da abubuwan da zasu faru nan gaba.
Gwamnatin tarayya a ranar Laraba data gabata ta sauya sunan ma’aikatar sufurin jiragen sama zuwa ma’aikatar sufurin jiragen sama da na sararin samaniya,Punch ta rawaito.
Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika ya ce zirga-zirgar jiragen sama da sararin samaniya suna da alaka da juna kuma Najeriya na da bukatar ta fito da manufofinta don daidaitawa da abubuwan da zasu faru nan gaba.
KARANTA WANNAN LABARIN: APC Ta Kafa Kwamitin Mutane 11 Da Zai Binciki Ayyukan Cin Amanar Jam’iyyar
Ministan ya bayyana hakan ne a wajen taron majalisar zartarwa ta tarayya da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta, a Abuja.
Sirika ya bayyana cewa canjin ya zama da amfani saboda yana cikin jerin keɓaɓɓu.
Sai dai ya ci gaba da cewa, makomar harkokin sufurin jiragen sama ta samu ci gaba ta yadda harkokin sufurin jiragen sama da sararin samaniyar suka hade kuma Najeriya na da bukatar ta fito da tsare-tsare don daidaitawa da abubuwan da zasu faru nan gaba.
Ministan ya kara da danganta wannan ci gaban da kafa Jami’ar Aerospace and Aviation University a Abuja
A wani labarin kuma,Dangana: Doguwa,Jiga-Jigan APC 2 Sun Hakura da Kujerar Majalisa, Sun Bayyana Dan takararsu
Shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai, Ado Doguwa ya janye daga neman takarar shugabancin majalisar
wakilai ta 10 tare da amincewa da Abbas
Doguwa ya jagoranci wasu ‘yan takara biyu Abubakar Makki da Tunji Oluwuyi da suka janye daga takarar a ranar Laraba.
A baya dai Doguwa ya bi sahun wasu masu neman kafa kawance don kalubalantar Abbas.