Shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai, Ado Doguwa ya janye daga neman takarar shugabancin majalisar
wakilai ta 10 tare da amincewa da Abbas
Doguwa ya jagoranci wasu ‘yan takara biyu Abubakar Makki da Tunji Oluwuyi da suka janye daga takarar a ranar Laraba.
A baya dai Doguwa ya bi sahun wasu masu neman kafa kawance don kalubalantar Abbas.
Shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai, Ado Doguwa ya yi murabus daga neman takarar shugabancin majalisar wakilai ta 10 tare da amincewa da Tajudeen Abbas,Daily Post ta rawaito.
Doguwa ya jagoranci wasu ‘yan takara biyu Abubakar Makki da Tunji Oluwuyi da suka janye daga takarar a ranar Laraba a wani taro da kungiyar hadin gwiwa ta shirya.
KARANTA WANNAN LABARIN: ACF Ta Nada Tsohon Minista A Matsayin Sabon Shugabanta
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa jam’iyyar APC mai mulki ta amince da Abbas da Ben Kalu a matsayin shugaban majalisar da mataimakinsa, lamarin da ya haifar da zanga-zanga a tsakanin ‘yan takarar.
A baya dai Doguwa ya bi sahun wasu masu neman kafa kawance don kalubalantar Abbas.
Duk da haka, a cikin wani abin mamaki, yanzu ya janye.
A jawabinsa ya bayyana cewa ba zai iya adawa da jam’iyyar ba.
A wani labarin kuma, Buhari Ya Samarwa Yan Najeriya Miliyan 12 Aikin Yi A Bangaren Noma – Garba Shehu
Babban mataimaki ga shugaban kasa Muhammadu Buhari kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, Garba Shehu ya bayyana adadin ayyukan yi da gwamnati mai ci ke samarwa a fannin noma abin a yaba ne.
A cewar Shehu, gwamnatin Buhari ta yi nasarar samar da sabbin guraben ayyukan yi miliyan 12 a fannin noma kadai.