- Kungiyar kwadago NLC ta yi fatali da taron da gwamnatin tarayya ta kira domin tattauna batun cire tallafin Fetur.
- Ma’aikatan wutar lantarkin sun sha alwashin shiga yajin aikin tare da jefa al’ummar kasar cikin halin kaka-nika-yi.
- Kungiyar ta dage cewa ba za ta yi wata tattaunawa da wakilan gwamnati ba, sai an kafa tawaga ta gaskiya.
A ranar Lahadi ne kungiyar kwadago ta Najeriya ta yi watsi da taron da gwamnatin tarayya ta kira domin tattauna batun cire tallafin fetur da kuma karin farashin man fetur a fadin kasar,kamar yadda Punch ta rawaito.
Kungiyar ta dage cewa ba za ta yi wata tattaunawa da wakilan gwamnati ba, sai an kafa tawaga ta gaskiya.
KARANTA WANNAN: Gwamnatin Kano Ta Kori Jami’an Dake Kula Da Cibiyoyi Hajji, Ta Rusa Otal
Sai dai jami’an kungiyar ‘yan kasuwan sun halarci taron wanda ya biyo bayan tattaunawar da suka yi da kungiyar NLC a fadar shugaban kasa da ke Abuja, a makon jiya, wadda ta kare batare da cimma wata matsaya ba.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ma’aikatan wutar lantarkin suka sha alwashin shiga yajin aikin tare da jefa al’ummar kasar cikin halin kaka-nika-yi, domin nuna adawa da cire tallafin man fetur da gwamnatin Bola Tinubu ta yi.
Ma’ajin kungiyar ta NLC, Hakeem Ambali, ya tabbatar da matakin da kungiyar ta dauka na kauracewa taron wanda ya biyo bayan taron da aka yi a ranar Laraba kan cire tallafin man fetur.
A yayin taron da ya samu halartar Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele, Manajan Darakta na Kamfanin Mai na Najeriya Mele Kyari, Dele Alake, da sauran su, NLC ta dage kan sauya farashin famfon mai da aka yi a tsakanin N488 zuwa N540 kankowacce lita.
Bayan rugujewar tattaunawar, NEC ta yanke shawarar shiga yajin aikin a taron data gudanar a ranar Juma’ar da ta gabata a duk fadin kasar.
A lokacin da yake zantawa da jaridar PUNCH a ranar Lahadi, Ambali ya bayyana cewa kamar TUC, an gayyaci kungiyar ta NLC domin gudanar da wani taro a fadar gwamnatin dake Abuja bayan taron da aka yi a baya wanda ya kawo karshe cikin rashin jituwa.
Ya kara da cewa kungiyar ba ta halarci tattaunawar ba saboda wakilan gwamnati ba su da hurumin tattaunawa da shugaban kasar.
“Taro ne da aka dakatar, wanda ya biyo bayan taron na karshe. Duk da haka, NLC ta dage cewa za mu kasance a shirye don tattaunawa da tawagar da ke da haƙƙin shugaba Tinubu.”
Da yake karin haske kan kauracewa zaman da NLC ta yi, shugaban kungiyar na kasa, Joe Ajaero, ya ce taron ba shi da wani tasiri ga majalisar.
NLC Ta Caccaki Gwamnatin Tarayya
Da yake magana a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise a ranar Lahadi, Ajaero ya ce, “Menene amfanin taron na yau? Tun a daren ranar Talata, na yi wata ganawa da shugaban TUC da wasu jami’an gwamnati.
“Na gaya wa manajan darakta na NNPCPL cewa duk wani yunkuri na kara farashin famfo za a dauki shi a matsayin yaki.
“Sun ci gaba da sanarwa. Muka ce su koma yadda ake tattaunawa domin a ci gaba da tattaunawa amma har yanzu ba su yi hakan ba. To me za mu je muyi a wajen taron mu yi?
A wani labarin kuma, Mataimakin Shugaban Kasa Shettima, Zulum da Buni Sun Halarci Jana’izar Tsohon Sakataren Gwamnatin Borno
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettina da wasu mashahuran mutane sun jagoranci zuwa wajen jana’izar tsohon sakataren gwamnatin Borno Usman Jidda Shuwa.
Alhaji Usman Jidda Shuwa ya rasu a ranar Asabar 3 ga watan Yuni 2023, yana da shekaru 65 a duniya.
Shuwa ya rike mukamin Sakataren gwamnati daga shekarar 2015 zuwa 2019 a lokacin Gwamna Kashim Shettima da kuma daga shekarar 2019 zuwa 2023 a karkashin Gwamna Zulum.