Jihar Zamfara ta samu mutum 21 masu dauke da cutar shan inna type 2 (CVDPV2) daga watan Janairu zuwa yau wanda masana suka dora alhakin matsalar tsaro da ke addabar jihar.
Shugaban Kwamitin Sarakunan Gargajiya na Arewa Mai Martaba Sarkin Argunge Samaila Mera ne ya bayyana haka, a wani taro na kwana daya da shugabannin gargajiya na al’ummar dake Jihar Zamfara, wanda aka gudanar a Gusau ranar Talata, Daily Post ta rawaito.
KARANTA WANNAN: Da Dumi-Dumi: Sarki Sanusi Ya Gana Da Jagororin Juyin Mulkin Jamhuriyar Nijar
A cewarsa, cutar shan inna mai nau’in type 2 da ta faro daga jihar Zamfara tuni ta kama yara 50 a kasar nan, daga cikin mutane 21 sun kamu da cutar a jihar, inda ya ce jihar ta shafi jihohi 26 na kasar nan da kuma wasu kasashen Afrika 29.
A cewarsa: “Saboda kalubalen tsaro, jihar ce ta fi kowacce yawan masu fama da cutar shan inna a kasar nan saboda rashin isa ga mafi yawan yankunan karkara domin yi musu rigakafi.
“Halin da ake fama da shi na matsalar tsaro a jihar ya sanya damar shiga al’ummomi zuwa ga yara da dama ya zama mai wahala ko kuma ba zai yiwu ba.
“Haka kuma ya haifar da barazanar barkewar cututtukan da za a iya rigakafi musamman cutar shan inna da aka samu ta hanyar alluran rigakafin. Don haka, jihar ce ta fi kowace kasa nauyi a kan cutar.”
Sarkin ya ci gaba da bayanin cewa, bayan tattaunawa dalla-dalla kan rahoton daga Zamfara, taron ya yi nuni da cewa, ana samun irin wannan yanayi a jihohin Sokoto, Kebbi, Katsina, Kaduna da kuma Neja.
Ya jaddada cewa, an gudanar da taron ne domin gano adadin wuraren da ba a isa ba saboda rashin tsaro.
A jawabin rufe taron, babban daraktan kuma babban jami’in hukumar kula da lafiya matakin farko na kasa, Dakta Faisal Shuaibu ya ce makasudin taron shi ne nemo hanyoyin da za a bi domin dakile yaduwar cutar shan inna da ke yaduwa nan da watan Disambar wannan shekara.
Ya ce hukumar za ta yi kokarin tuntubar dukkan yaran jihar domin a yi musu allurar rigakafin cutar shan inna ko da kuwa da matsalar tsaro.
“Dole ne mu karfafa haɗin gwiwa da hukumomin tsaro don samar da amintattun hanyoyin ma’aikatan kiwon lafiya,” in ji shi.
A wani labarin kuma, An Lalata Haramtattun Matatun Mai 100, An Kama Mutane 200 Da Ake Zargi — NSCDC
Babban kwamandan hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya, Ahmed Audi, a ranar Laraba ya bayyana cewa an lalata matatun mai da suke ba bisa ka’ida ba da basu gaza kasa da 100 ba tare da kama mutane 200 cikin shekaru biyu.
Hakan ya faru ne yayin da CG ya bukaci jami’an da su kara himma wajen magance satar mai da lalata bututun mai.