Babban kwamandan hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya, Ahmed Audi, a ranar Laraba ya bayyana cewa an lalata matatun mai da suke ba bisa ka’ida ba da basu gaza kasa da 100 ba tare da kama mutane 200 cikin shekaru biyu.
Hakan ya faru ne yayin da CG ya bukaci jami’an da su kara himma wajen magance satar mai da lalata bututun mai.
KARANTA WANNAN: Da Dumi-Dumi: Shugaba Tinubu Ya Sanya Labule da Wike, El-Rufai a Villa
Audi ya bayyana haka ne a taron CG na biyu da aka gudanar a Abuja.
Da yake magana game da kokarin da rundunar ta yi, CG ya ce, “Sama da matatun mai 100 da suke ba bisa ka’ida ba an lalata su kuma an kama sama da mutane 200 da ake zargi a cikin shekaru biyu.”
Ya tunatar da ma’aikatan kalubalen da ke gabansu da kuma bukatar magance barazanar tsaro yadda ya kamata.
Ya ce, “Muna kuma bukatar mu kara zage damtse wajen kare muhimman kadarorin kasa da ababen more rayuwa, da magance kalubalen satar mai da fasa bututun mai, da tabbatar da kare manoma da filayen noma don tabbatar da samar da abinci, da kare kayayyakin wutar lantarki, da hanyoyin sadarwa da sassan sufuri tare da mai da hankali kan abubuwan more rayuwa na layin dogo da sauransu.
“Dole ne mu fara samar da sabbin dabaru don magance matsalar rashin tsaro a kasar. Ta wannan hanyar, rundunar ta ba da fifikon bayar da horo da sake horarwa, da kuma sayan kayan aiki na zamani da na sadarwa a kudurinmu na kara inganta karfin rundunar.”
A wani labarin kuma, Gwamnatin Legas Ta Fara Wani Yunkurin Maida Matasa Masu Dogaro Da Kawunan Su
Gwamnatin jihar Legas ta sake tabbatar da cewa ta samar da tsare-tsare da ke da nufin ganin matasan jihar sun zama masu dogaro da kai.
Babbar Sakatariyar ma’aikatar matasa da ci gaban al’umma Toyin Oke-Osanyintolu ce ta sanar da hakan yayin da take ƙaddamar da bude shirin horar da ‘yan kasuwa mai taken “Business Amplifier Clinic” horon kwanaki 3 ga zababbun matasa ‘yan kasuwa a matsayin wani bangare na shirin samar da ayyuka don bikin ranar Matasa ta Duniya.