- Kasar Sin ta ba da gudummawar dalar Amurka miliyan daya don tallafawa shirin ilimi na Hukumar Ba da Agaji da Ayyuka ta Falasdinu a Gabas ta Tsakiya
- Tallafin zai amfanar da yara ‘yan gudun hijira dubu 5,300 a makarantun UNRWA guda biyar
- Kusan duk kuɗaden da Hukumar take samu yana fitowa ne daga gudummawar son rai
Kasar Sin ta ba da gudummawar dalar Amurka miliyan daya don tallafawa shirin ilimi na Hukumar Ba da Agaji da Ayyuka ta Falasdinu a Gabas ta Tsakiya (UNRWA).
A cikin wata sanarwa da ofishin ya fitar, ya ce, shugaban ofishin Jamhuriyar kasar Sin a kasar Falasdinu, Zeng Jixin, ya rattaba hannu kan yarjejeniyar bayar da gudummawar da Karim Amer, darektan hadin gwiwa na UNRWA.
KARANTA WANNAN: Yanzu-Yanzu: Manyan Hafsoshin tsaron ECOWAS na Cigaba da Tattaunawa Kan Makomar Nijar
Tallafin zai amfanar da yara ‘yan gudun hijira 5,300 a makarantun UNRWA guda biyar a fadin zirin Gaza, in ji UNRWA.
Zeng ya kara da cewa, kasar Sin ta amince da kuma yaba wa aikin UNRWA, kuma tana ba da taimako gwargwadon ikonta na tallafa wa UNRWA wajen sauke nauyin da aka dora mata.
Ya ce, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da kasashen duniya don ba da gudumawa mai kyau don samun cikakkiyar hanyar warware matsalolin Palasdinu tare da tabbatar da zaman lafiya da tsaro da wadata a yankin gabas ta tsakiya.
Amer ya godewa kasar Sin saboda gudummawar da ta bayar, ya kuma yaba wa kasar Sin a matsayin “abokiyar hulda mai kima da girma” ga UNRWA.
Amer ya ce, “Saboda dawwamammiyar goyon bayan masu ba da taimako kamar gwamnatin kasar Sin UNRWA za ta iya ba da hidima ga ‘yan gudun hijirar Falasdinu a yankin Gabas ta Tsakiya.”
An kafa ta a cikin shekarar 1949, UNRWA tana ba da izinin ba da agaji ga ‘yan gudun hijirar Falasdinu.
Kusan duk kuɗaden da take samu yana fitowa ne daga gudummawar son rai.
A wani labarin kuma,Da Dumi-Dumi: Gwamnan PDP Ya Ayyana Muhimmiyar Ranar Hutu a Jihar Sa
Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya amince da ranar 20 ga watan Agusta na kowace shekara a matsayin ranar Isese
A shekarun baya mabiya addinin gargajiya a jihar sun bukaci suma tasu ranar hutu ta daban
Wannan dai shine karo na farko da gwamnan ya ta ba bada ranar hutun jama’a a jihar
Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya amince da ranar 20 ga watan Agusta na kowace shekara a matsayin ranar Isese a jihar.
Makinde ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a.