- A halin yanzu dai hafsoshin tsaron kasashen yammacin Afirka na ci gaba da tattaunawa a rana ta biyu a kasar Ghana kan yiwuwar kutsawa da makami don maido da mulkin farar hula a jamhuriyar Nijar
- Idan har yunkurin diflomasiyya na kawo karshen juyin mulkin da aka yi a Nijar ya ci tura za’ayi amfani da karfin soji
- Ana sa ran hafsoshin tsaron za su sanar da duk wani mataki na gaba a bikin rufe taron
A halin yanzu dai hafsoshin tsaron kasashen yammacin Afirka na ci gaba da tattaunawa a rana ta biyu a kasar Ghana kan yiwuwar kutsawa da makami don maido da mulkin farar hula a jamhuriyar Nijar idan har yunkurin diflomasiyya na kawo karshen juyin mulkin da aka yi ya ci tura, Punch ta rawaito
A cewar Al Jazeera, ana sa ran hafsoshin tsaron za su sanar da duk wani mataki na gaba a bikin rufe taron da karfe 4 na yamma.
KARANTA WANNAN: Da Dumi-Dumi: Gwamnan PDP Ya Ayyana Muhimmiyar Ranar Hutu a Jihar Sa
Dakarun kungiyar hadin kan tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka a rana daya da ta gabata sun yi alkawarin shiga cikin rundunar da za ta maido da dimokuradiyya a Nijar bayan hambarar da shugaban kasar Mohamed Bazoum tare da tsare shi.
Dukkanin kasashe mambobin kungiyar, in ban da wadanda ke karkashin mulkin soja da kuma Cape Verde, sun amince a wani taro a Accra, babban birnin kasar Ghana, a ranar Alhamis da ta gabata, da su kaddamar da rundunar ta musamman, a matsayin mataki na karshe na maido da dimokuradiyya a Nijar.
Shugabannin kungiyar ECOWAS na gudanar da wani taro na kwanaki biyu a Accra babban birnin kasar Ghana, domin daidaita bayanai kan yuwuwar sojojin da za su dawo da Bazoum kan karagar mulki, idan aka ci gaba da tattaunawa da shugabannin da suka yi juyin mulki ya ci tura.
A wani labarin kuma,Yobe: NDLEA ta Nada Shugaban NUJ a Matsayin Jakadan Yaki da Miyagun Kwayoyi
Shugaban kungiyar ‘yan jaridu na jihar Yobe kwamared Rajab Mohammed, ya bayyana cewar da akwai bukatar kulla dankantar aiki tsakanin kafafen yada labarai da hukumar kula da safaran miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA .
Shugaban ya baiyana hakan ne a yayin da kungiyar ta NUJ ta kai wa kwamandan hukumar na jihar Yobe ziyarar bangirma a offishin su dake hanyar Gujba a Damaturu.