- Yan sandan kasar Birtaniya sun gurfanar da tsohuwar ministar albarkatun man fetur, Diezani Alison-Madueke da laifin karbar cin hanci
- Tsohuwar ministar ta kasance jigo a gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, inda ta rike mukamin ministar albarkatun man fetur
- Ana zargin Diezani Alison-Madueke ta yi amfani da karfinta a Najeriya tare da karbar tukwicin kudi kan bayar da kwangiloli na miliyoyin Fam
‘Yan sandan kasar Britaniya sun gurfanar da tsohuwar ministar albarkatun man fetur, Diezani Alison-Madueke a ranar Talata da laifin karbar cin hanci, inda ta ce suna zargin ta karbi cin hanci da rashawa a matsayin ta na bada kwangilar man fetur da iskar gas na miliyoyin fam.
Alison-Madueke mai shekaru 63, ta kasance jigo a gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, inda ta rike mukamin ministar albarkatun man fetur daga shekarar 2010 zuwa 2015.
KARANTA WANNAN: Da Dumi-Dumi: Shettima Ya Shilla Kasar Waje Domin Wakiltar Tinubu a Wani Muhimmin Taro
Ta kuma rike mukamin shugabar kungiyar kasashe masu arzikin man fetur.
“Muna zargin Diezani Alison-Madueke ta yi amfani da karfinta a Najeriya tare da karbar tukwicin kudi kan bayar da kwangiloli na miliyoyin Fam.
“Wadannan tuhume-tuhumen wani ci gaba ne a cikin abin da ya kasance cikakken bincike na kasa da kasa,” in ji Andy Kelly, Shugaban Sashen Cin Hanci na Duniya na Hukumar Laifuka ta Kasa.
Hukumar ta NCA ta ce ana zargin Alison-Madueke da cin gajiyar akalla fam 100,000 na tsabar kudi, motoci, jiragen sama masu zaman kansu, kayayyakin alfarma ga danginta, da kuma yin amfani da wasu kadarori na Landan.
Har ila yau, tuhume-tuhumen da ake yi mata na dalla-dalla game da ladan kudi da suka hada da kayan daki, aikin gyare-gyare da kuma ma’aikata don kadarorin, biyan kudaden makaranta masu zaman kansu, da kyaututtuka daga manyan shagunan zane irin su kayan adon cartier da kayayyakin Louis Vuitton, in ji NCA.
‘Yan sandan Burtaniya sun ce a halin yanzu tana zaune a St John’s Wood, dake a yammacin London, kuma za ta bayyana a Kotun Majistare ta Westminster a ranar 2 ga watan Oktoba, 2023.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa Alison-Madueke wadda hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ke tuhumar ta tun bayan da ta bar ofis, tana fuskantar tuhumar cin hanci da rashawa amma ta musanta zargin.
A watan Oktobar shekarar 2022, Mai shari’a Mobolaji Olajuwon na babbar kotun tarayya da ke Abuja ya ba da umarnin a kwace kadarori biyu na Abuja da wasu motoci na alfarma guda biyu mallakar Alison-Madueke, ga gwamnatin tarayya.
Kaddarorin biyu suna a Lamba 1854 Mohammed Mahashir Street da lamba 6, Aso Drive a babban titin Asokoro da Maitama dake Abuja, kuma an kiyasta kudinsu ya kai dala $2,674,418 da kuma Naira miliyan N380m.
Motocin alfarmar dai sun hada bakar salon BMW ne mai casis lambar B8CV54V66629 da lambar rijista RBC155 DH da wata bakar salon Jaguar mai casis lamba SAJAA.20 GRDMv43376 wadda darajarta takai naira miliyan N36m.
Alkalin ya bayar da umarnin kwace kadarorin ga gwamnatin tarayya a lokacin da ya yanke hukunci kan bukatar da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta yi, mai lamba 1122/2021 da kuma kara mai lamba 1123/2021, inda ya bukaci a kwace kadarorin na karshe.
Hukumar ta EFCC a cikin wata sanarwa da wakilinmu ya samu ta ce hukumar a ranar 29 ga watan Nuwambar shekarar 2021, ta samu nasarar kwace kadarorin na wucin gadi a wani hukunci na daban da tsohon jam’iyyar ya shigar a ranar 27 ga watan Satumbar shekarar 2021, wanda ya roki kotu da ta ba da umarnin kwace kadarorin na wucin gadi kan dalilan da suka dace na cewa kudaden haram ne.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Da yake bayar da umarnin kwace kadarorin na wucin gadi, Mai shari’a Olajuwon ya umarci hukumar EFCC da ta wallafa wata sanarwa a wata jarida ta kasa, inda ta gayyaci duk wanda ke da sha’awar kadarorin domin ya nuna dalilin da ya sa a karshe ba za a ba da su ga gwamnatin tarayyar Najeriya ba.
Sakamakon haka kotun ta dage zaman har zuwa ranar 22 ga watan Janairun shekarar 2022, domin samun rahoto.
Tsohuwar Minista Alison-Madueke Ta Shigar Da Karar EFCC
Sai dai a watan Mayu, 2023, Alison-Madueke ta shigar da kara a kan hukumar EFCC da kuma ofishin babban mai shari’a na tarayya kan abin da ta kira yunkurin karya da mugun nufi na “shafa mata fenti a matsayin mai laifin gama-gari”.
Shari’ar da aka shigar a babbar kotun tarayya da ke Abuja, mai lamba CV/6273/2023, ta samu sa hannun lauyanta, karkashin jagorancin Mista Mike Ozekhome, SAN.
Tana da EFCC da AGF a matsayin wadanda ake tuhuma na daya da na biyu.
Alison-Madueke ta bukaci a biya ta Naira miliyan 100 a matsayin diyya kan “zargin karya da yada labaran karya” da EFCC ta rubuta mata.
Ta kuma kara da cewa dole ne EFCC ta nemi afuwa a kalla a cikin jaridun kasar nan guda uku kan “Batancin da aka yi mata”.
Hukumar EFCC, a ranar 8 ga watan Agustar shekarar 2017, ta fitar da wata fallasa mai suna, ‘EFCC ta gano Naira biliyan N47.2bn sannan kuma da Dala miliyan $487.5m ga tsohuwar Minista Diezani Alison-Madueke’, inda ta zargi tsohuwar ministar da zamba da karkatar da kudade.
Alison-Madueke Ta Bar Najeriya Jim Kadan Bayan Ta Bar Mulki A Shekarar 2015.
Jim kadan bayan fitar da hukumar EFCC ta kama wasu makudan kudade da wasu kadarori da suka hada da kayan ado da gidaje da ake alakanta su da ita, an kuma yi awon gaba da su ga gwamnatin tarayya.
Alison-Madueke, a karar da ta shigar da EFCC da AGF, ta musanta zargin, inda ta kara da cewa, wallafar da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta fitar an yi shi ne da ‘mugun rubutu da/ko kuma aka sa a rubuta ko wallafa wa duniya gaba daya’.
A cikin sanarwar, Alison-Madueke, ta bakin lauyanta, Ozekhome, ta ce dalilin da ya sa ta bar kasar a ranar 22 ga watan Mayun shekarar 2015, shi ne saboda an gano tana da cutar kansar nono mafi tsanani – Triple Negative Cancer – kuma ta kasance cikin gaggawa aka garzaya da ita zuwa Ingila domin gudanar da wani muhimmin aikin jinya’.
Alison-Madueke ta ci gaba da cewa, ‘Ba a gano ko da kuwa dala miliyan 72.8 da aka danganta da ita a bankin Fidelity ba.
“Mai shigar da karar (Alison-Madueke) ya bayyana cewa sabanin maganar ban dariya da wanda ake kara na 1 ya yi cewa an gano kudaden da suka kai Naira Biliyan N47.2bn da kuma dala miliyan $487.5m, $2.5bn, $72.8m, da dai sauransu, an same su ne a gidan mai da’awar da asusun banki abin dariya ne domin babu wani gida da zai iya ajiye irin wadannan makudan kudade sai babban bankin Najeriya; haka kuma bankuna su rike irin wadannan kudade ba tare da sanar da hukumomin da suka dace ba.”
A wani labarin kuma, Ku Shirya Tunkarar Ƴan Bindiga – Kwamishinan Ƴan Sanda Ga Jami’ai
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Katsina, Abubakar Musa, a ranar Litinin din nan, ya bukaci sabbin jami’an da aka kara ma girma a jihar da su yi aiki tukuru, kuma su kasance a shirye don tunkarar ‘yan bindiga da sauran masu aikata laifuka a jihar.
An yi hakan ne domin yakar tashe-tashen hankula a sassan kananan hukumomin jihar.