Ku Shirya Tunkarar Ƴan Bindiga – Kwamishinan Ƴan Sanda Ga Jami’ai
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Katsina, Abubakar Musa, a ranar Litinin din nan, ya bukaci sabbin jami’an da aka kara ma girma a jihar da su yi aiki tukuru, kuma su kasance a shirye don tunkarar ‘yan bindiga da sauran masu aikata laifuka a jihar.
An yi hakan ne domin yakar tashe-tashen hankula a sassan kananan hukumomin jihar.
KARANTA WANNAN LABARIN:Juyin Mulki: El-Rufai Ya Magantu Kan ECOWAS da Jamhuriyar Nijar
Jami’an da aka yi wa ƙarin girma su 161, inda aka daga darajar sufeto ‘yan sanda zuwa mataimakin Sufeto na ‘yan sanda (ASP) a hedikwatar rundunar, Katsina.
Kwamishinan ‘yan sandan a lokacin da yake ba su shawarar su guji cin hanci, ya umarce su da su yi aiki tukuru da kuma guje wa yaudarar ‘yan kasa.
“kimanin ƴan sanda 161 ne hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda ta basu karin girma ta hanyar shawarar mukaddashin sufeto-janar na ‘yan sanda.
“Mun tuhume su da su kasance masu aiki tukuru kuma a shirye suke su fuskanci ‘yan bindiga da sauran masu aikata laifuka a sassansu.
“Ba da jimawa ba, za mu tura su masu da mukamai masu nauyi. Wasu daga cikinsu muna mai da su jami’an tashoshi a galibin kauyukan da ke fama da matsalar ‘yan fashi.
“A cikin manufofina lokacin da na kai rahoto ga rundunar, ba na son wani ya nemi kudi ya zo ya ce yana son CP ko wani jami’ina. Domin su yi aikinsu da kyau da inganci kuma kada su damfari wani mutum ko dan kasa a inda suke hidima, duk wanda aka samu yana so za a hukunta shi da gaske,” inji shi.
A wani labarin kuma:Juyin Mulki: El-Rufai Ya Magantu Kan ECOWAS da Jamhuriyar Nijar
Yayin da farashin kayan abinci ke ci gaba da tashin gwauron zabi, sabon ministan noma da samar da abinci, Sanata Abubakar Kyari, a ranar Litinin, ya bayyana cewa daya daga cikin manyan matsalolin da ke addabar kasar nan ita ce yunwa, ya kuma sha alwashin magance ta.
Kyari ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi aiki a hedikwatar ma’aikatar da ke Abuja tare da karamin ministan noma da samar da abinci, Sanata Aliyu Abdullahi.