Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje, a ranar Talata, ya ziyarci gwamnan jihar Ondo, Mista Rotimi Akeredolu, inda ya yaba masa bisa kyakkyawan shugabancin da yake samarwa al’ummar jihar.
Shugaban ya kai ziyarar ne tare da sakataren jam’iyyar na kasa Sanata Surajudeen Ajibola Bashiru; Mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa (Kudu maso Yamma), Mista Isaac Kekemeke; Mataimakin sakataren jam’iyyar na kasa, Sir Festus Fuanter; mataimakin sakataren kudi na kasa, Hamma Kumo; da sauransu.
KARANTA WANNAN: Da Dumi-Dumi: Nasarawa United ta Nada Sabon Koci
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamnan, Richard Olatunde, ya fitar a Akure, ranar Talata.
Da yake jawabi tare da maziyartan, Akeredolu ya bayyana kwarin gwiwar Ganduje wajen ciyar da jam’iyyar gaba da hadin kai. Ya bayyana cewa, dimbin gogewar da Ganduje ya samu daga yin wa’adi biyu a matsayin gwamnan jihar Kano, ya ba shi wadatattun kayan aikin da zai jagoranci jam’iyyar zuwa ga gagarumin ci gaba.
Ya ce, “Na gode wa Allah da ya ba mu kyautar rai. Ni da kaina ina so in nuna godiyata cewa ina raye kuma cikin koshin lafiya. Mun dawo da yardar Allah.
“Ina so in gode muku duka da kuka zo. Na san cewa Ubangiji ya amsa addu’ata, amma ina bukatar ƙari. Shugabana, na san kai mai iyawa ne, kuma za ka iya dogaro da goyon bayana kowane lokaci. Jam’iyyar ta ci gaba, kuma dole ne ta ci gaba da kula da harkokin kasar baki daya.”
Tun da farko, Ganduje ya ce gwamnan na da matukar muhimmanci ga jam’iyyar da kuma kasa. Ya kara da cewa ba za su iya mantawa da irin kyakkyawan shugabanci da Akeredolu yake yi wa Ondo da kasar nan ba.
“Mun zo nan ne kawai don ganin ku bayan dadewar da kuka yi bakwa kasar. Ka ba mu muhimmanci sosai a APC da kasa. Mun yi addu’a sosai don samun lafiyar ka.
“Ba za mu manta da kyakkyawan shugabanci da kuke yi wa jihar Ondo da ma Najeriya baki daya ba. Lokacin da ɗayanmu ya fuskanci ƙalubalen lafiya, mu ma muna jin hakan. Mun zo da Bishop din mu ne domin mu yi muku addu’o’in samun lafiya,” in ji Ganduje.
Ya sanar da gwamnan cewa kwamitin gudanarwa na jam’iyyar na kasa ya yi gyara a lokacin da ba ya nan.
“Ba tare da ku ba, an gyara kwamitin gudanarwa na kasa. Shugaban jam’iyyar na kasa da sakataren jam’iyyar na kasa duk sun yi murabus. Kafin wannan, akwai gibi saboda murabus ko kuma mace-mace.
“Tafiyar shugaban ta bar wani gagarumin gibi, kuma hukumar ta NEC ta ga bukatar cike muhimman mukamai. Cikin ikon Allah ni ne sabon shugaban jam’iyyar, kuma Bashiru shi ne sabon Sakatare. Yanzu dai kwamitin gudanarwa na kasa ya fara aiki tukuru,” inji Ganduje.
Akeredolu ya dawo kasar ne kwanaki kadan da suka wuce daga hutun jinya da ya yi a kasar Jamus, kuma tuni ya ke a gidansa da ke Ibadan a jihar Oyo.
A wani labarin kuma, Kakakin Majalisa Abbas Ya Jajanta Wa Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa a Legas
Kakakin Majalisar Wakilai, Honarabul Abbas Tajudeen, ya bayyana alhininsa kan mutuwar mutum daya sakamakon ambaliyar ruwa da ta afkawa wasu sassan mazabar Kosofe dake Jihar Legas.
Kakakin majalisar a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai Musa Krishi ya fitar, ya kuma bayyana damuwarsa kan yadda ambaliyar ta raba mutane sama da 2,000 da gidajensu.