- Jam’iyyar PDP ta yi watsi da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zabe ta yanke na zaben gwamnan jihar Benue
- Kotun zaben Gwamna ta yi watsi da karar da jam’iyyar PDP da dan takararta na gwamna suka shigar kan jam’iyyar APC
- Jam’iyyar ta umurci lauyoyin ta da su daukaka kara kan hukuncin da aka yanke a kotun daukaka kara cikin wa’adin da doka ta kayyade
Jam’iyyar PDP ta yi watsi da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zabe ta yanke na zaben gwamnan jihar da ta tabbatar da zaben Rev Fr Hyacinth Alia a matsayin gwamnan jihar Benue.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rahoto cewa Kotun sauraren kararrakin zaben Gwamna da ke zamanta a Makurdi, a ranar Asabar, ta yi watsi da karar da jam’iyyar PDP da dan takararta na gwamna, Titus Uba, suka shigar kan zaben Alia na jam’iyyar APC.
KARANTA WANNAN: Burina Shi Ne In Goyi Bayan Shugaba Tinubu – Gwamna Bello
Kotun ta yanke hukuncin cewa koken na PDP bai dace ba.
Jam’iyyar PDP reshen jihar Benue ta yi watsi da hukuncin kotun a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaranta, Bemgba Iortyom ya fitar.
Sanarwar ta kara da cewa, “Bayan nazarin hukuncin da tawagar lauyoyin ta, PDP ta yi imanin cewa ba ta cika ka’idojin adalci ba, kuma ba ta dace da dokokin zabe ba.
“Saboda haka jam’iyyar ta umurci lauyoyin ta da su daukaka kara kan hukuncin da aka yanke a kotun daukaka kara da ke Abuja cikin wa’adin da doka ta kayyade.
“Jam’iyyar mu mai girma tana kira ga dimbin magoya bayanta a fadin jihar nan da su kwantar da hankulansu kuma su jajirce bisa imanin cewa duk da tafiyan adalci na iya dadewa, amma a karshe za a cimma burin dawo da kujerar Gwamna”.
A wani labarin kuma, Rikici: Sama da mutane 81,000 ne suka shiga Habasha daga Sudan – Majalisar Dinkin Duniya
Adadin mutanen da suka isa Habasha sakamakon rikicin Sudan ya kai 81,095 a cewar hukumar kula da shige da fice ta Majalisar Dinkin Duniya.
Ya zuwa ranar 16 ga watan Satumba, jimillar mutane 81,095 da ‘yan gudun hijira, da ‘yan cira ni da masu neman mafaka daga Sudan da ke fama da rikici suka shiga makwabciyarta, Habasha, in ji hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta duniya, IOM.