Adamawa: Rikicin Manoma da Makiyaya ya yi sanadiyar mutuwar Mutane 305 cikin shekaru 5 – Babban Malamin Jami’a
Rikici tsakanin Makiyaya da Manoma ya yi sanadiyar mutuwar Mutane 305 a Jihar Adamawa cikin shekaru biyar kamar yadda wani Babban Malamin Jami’a mai bincike Dr. John Ngamsa ya bayyana.
Ngamsa mamba ne na kwamitin Jihar Adamawa kan rikicin Manoma da Makiyaya, Dr. John Ngamsa ya yi magana a wani taron tattaunawa da Kamfanin Ramo Multimedia Centre ta shirya a Yola.
Da yake tsokaci kan rahotannin kafafen yaɗa Labarai, Ngamsa wanda malami ne a Jami’ar Modibbo Adamawa Yola ya ce “Akalla mutane 305 ne aka kashe a rikicin da ya shafi Makiyaya da Manoma a Jihar Adamawa tsakanin shekarar 2016 zuwa 2021.
Wannan rikici na rashin hankali tsakanin Manoma da Makiyaya a yankin yana soma ne tun farkon shekarar 2000.
KARANTA WANNAN LABARIN:Na Gwammace in yi aiki Mai Tasiri Cikin wa’adi 1 da inyi Wa’adi 2 marar Amfani – Gwamnan Eno
Ya ƙara da cewa, rigingimun da Manoma da Makiyaya ke ci gaba da yi musamman a ƙaramar Hukumar Demsa ya yi sanadiyar salwantar rayuka da dukiyoyi da yawa.
Ngamsa wanda ya taɓa zama kwamishina a Gwamnatoci biyu da suka gabata a Jihar, ya danganta raguwar tashe-tashen hankula a cikin shekaru huɗu da suka gabata da yunkurin samar da zaman lafiya ga ƙoƙarin Gwamnan Jihar Adamawa Ahmadu Fintiri ya aiwatar, wanda ya ce ya yi duk abin da ya kamata domin sanya kwamitin Jihar Adamawa kan rikicin makiyaya da Manoma domin rikicin ya zama ruwan dare.
Ya ce kwamitin ya yi aiki tuƙuru don ganin an samar da tsari mai dorewa na zaman lafiya domin kare lafiyar mazauna Jihar Adamawa.
Ngamsa ya kuma jaddada cewa, magance rikice-rikice tsakanin Manoma da Makiyaya na da matuƙar Muhimmanci ga ci gaban Jihar da ma ƙasa baki ɗaya.
A wani labarin kuma:Najeriya Ce Alfaharin Kasashen Nahiyar Afirika-Shettima
Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, a ranar Juma’a, ya bukaci shugabannin majalisar dokokin kasar ta 10 da su rungumi mabambantan ra’ayoyi da kuma yin aiki domin dorewar dimokuradiyyar Najeriya.
Dimokradiyya na samun bunkasuwa idan muka yarda cewa kowace murya tana da kima in ji Mista Shettima a Ikot Ekpene, jihar Akwa Ibom, yayin da yake bayyana bude taron kwana biyu ga shugabannin majalisar dokokin kasar.