- Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya ce fursunoni sama da 4,000 ne ake tsare da su a cibiyoyin gidajen yari daban-daban a fadin kasar nan
- Adadin fursunonin da ake tsare da su a gidajen yarin zai ragu zuwa kashi 40 cikin 100 idan aka binciko wasu hanyoyin da ba na tsarewa ba
- Ma’aikatar tana aiki kan muhimman sauye-sauye da suka shafi ‘yan Najeriya
Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya ce fursunoni sama da 4,000 ne ake tsare da su a cibiyoyin gidajen yari daban-daban a fadin kasar nan saboda rashin iya biyan tarar da alkalai suka yi musu, Punch ta rawaito.
Wannan ya kasance kamar yadda ya koka da cewa sama da kashi 70 cikin 100 na yawan jama’ar da ke cibiyoyin kula da gyaran hali dake kasar nan suna jiran shari’a.
KARANTA WANNAN: Jihar Jigawa Ta Samu Mutane 91 da Ake Zargin Sun Kamu Da Cutar Mashako
Ya yi nuni da cewa adadin fursunonin da ake tsare da su a gidajen yarin zai ragu zuwa kashi 40 cikin 100 idan aka binciko wasu hanyoyin da ba na tsarewa ba kamar yadda dokar da ta tanada.
Wata sanarwa a ranar Asabar da ta fito daga bakin mai baiwa ministan shawara kan harkokin yada labarai, Alao Babatunde, ta ce ya yi magana ne a lokacin da jakadan Tarayyar Turai a Najeriya, Samuela Isopi, ya ziyarce shi a ofishinsa da ke Abuja.
A wani bangare na sanarwar an karanta cewa, “Sama da kashi 70 na fursunoni 79,000 suna jiran shari’a.
“Muna da fursunoni sama da 4,000 a wuraren saboda rashin biyansu tara daban-daban. Mun yi imanin za mu iya rage adadin fursunonin da ke cikin wuraren gidajen gyaran hali da tarbiyyar mu da kusan kashi arba’in idan muka yi la’akari da wasu hanyoyin da ba na tsarewa ba kamar yadda aka tanadar a cikin Dokar aiki ta gidan Gyaran hali da tarbiyya.”
Ministan ya bayyana cewa EU za ta iya tallafawa kasar wajen tura fasahar kere-kere da inganta gine-ginen kula da iyakoki a cikin kasar.
Ya ce, “Kungiyar Tarayyar Turai na da muhimmanci ga ci gaban zamantakewa da tattalin arzikin Nijeriya.
“Dangantakar mu da EU ta tarihi ce amma ba ta takaita ga goyon bayan kasashen biyu ba,” inji shi.
“Idan za mu iya magance laifuka da matsalolin ƙaura a Najeriya, Afirka za ta fi dacewa da ita. Saboda iyakoki, Afirka na tarayya da EU, matsalolinmu sun fi kowane yanki na duniya. Kuma, saboda mun himmatu wajen magance wannan, za mu binciko dukkan hanyoyin.”
Ministan ya bukaci EU da ta goyi bayan shirin Gwamnatin Tarayya na gudanar da binciken duk wasu cibiyoyin gidan gyaran hali da tarbiyya.
Tunji-Ojo ya yi nuni da cewa, ma’aikatar tana aiki kan muhimman sauye-sauye, musamman a fannonin da suka shafi takardun tafiye-tafiye da kuma canja wurin ilimi.
Ya kara da cewa, “Mun fara aikin ne domin warware matsalolin da ke tattare da aikace-aikacen fasfo na kasa da kasa. A yau, mun sami ci gaba mai yawa. Muna kuma aiki kan hanyoyin rage satar bayanan sirri. Muna son tabbatar da koren fasfo din ya dawo da alfahari da mutuncinsa.”
Tun da farko, jakadan ya baiwa ministar tabbacin goyon bayan kungiyar tarayyar turai, yana mai cewa kungiyar ta EU za ta ba da goyon bayan fasaha wajen tafiyar da al’amuran da suka shafi kaura ba bisa ka’ida ba tare da dakile safarar mutane.
A wani labarin kuma, PDP ta Yi Fatali da Hukuncin Kotun da ta Tabbatar da Nasarar Zaben Gwamna Alia
Jam’iyyar PDP ta yi watsi da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zabe ta yanke na zaben gwamnan jihar Benue
Kotun zaben Gwamna ta yi watsi da karar da jam’iyyar PDP da dan takararta na gwamna suka shigar kan jam’iyyar APC
Jam’iyyar ta umurci lauyoyin ta da su daukaka kara kan hukuncin da aka yanke a kotun daukaka kara cikin wa’adin da doka ta kayyade
Jam’iyyar PDP ta yi watsi da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zabe ta yanke na zaben gwamnan jihar da ta tabbatar da zaben Rev Fr Hyacinth Alia a matsayin gwamnan jihar Benue.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rahoto cewa Kotun sauraren kararrakin zaben Gwamna da ke zamanta a Makurdi, a ranar Asabar, ta yi watsi da karar da jam’iyyar PDP da dan takararta na gwamna, Titus Uba, suka shigar kan zaben Alia na jam’iyyar APC.